Tallafin Karatu Ya Kamata Gwamnati Ta Bawa Ɗalibai, Ba Bashi Ba – ASUU
Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta yi zargin cewa, shirin bada rancen kuɗaɗen karatu ga Ɗaliban Manyan Makarantu, da Gwamnatin ta ɓullo da shi, wani salo ne na ƙara azurta mamallakan Jami’o’i masu zaman kansu, da ke faɗin ƙasar nan.
Shugaban ƙungiyar ASUU na ƙasa, Farfesa Emmanuel Osodeke, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Christopher Piwuna, shi ne ya bayyana hakan, ya yin da ya ke zantawa da Ƴan Jaridu, a jihar Bauchi, a wani ɓangare na miƙa kuɗaɗen tallafin karatu ga Ɗaliban da ke karatun Digirin farko, a shiyyar ƙungiyar ta Bauchi, da ya gudana, a Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBU), da ke Yelwa, a ranar Asabar.
Piwuna, ya ce kamata ya yi ace tallafi Gwamnatin za ta bawa Ɗaliban, a madadin tace ta basu bashi.
Ya na mai cewar, “Tun daga farko, mun fahimci cewar Najeriya ba za ta iya ɗaukar nauyin Ilimi ba. Matsalolin da su ka dabai-baye tsarin ne ma ya sanya aka shigo da wannan shirin na bada bashi, baya ga kuɗaɗen da Jami’o’in ke cigaba da ƙarawa na Makaranta, sakamakon gazawar Gwamnati wajen ɗaukar nauyin Ilimin. Ya kamata dai ace Gwamnati ta kawo ƙarshen tazarar da ake samu wajen ɗaukar nauyin Jami’o’in nan.
“Mun yi Imanin cewar, da za a kyautata tsari, Gwamnati za ta iya ɗaukar nauyin Ilimin nan yadda ya dace. Daga abubuwan da mu ke ganin su na faruwa a baya-bayan nan, misali: yadda Ɗan Majalissar Wakilai ta ƙasa, wani sashe na alawus ɗinsa kawai ya kai Naira miliyan 160, babbar alama ce da ke nuna cewar, da ace Najeriya da gaske ta ke, to tabbas za ta iya ɗaukar nauyin Ilimi.”.
A jawabinsa, tun da farko kan tallafin karatun, da ƙungiyar ta miƙa ga kimanin Ɗalibai 19 a shiyyar ta Bauchi, Shugaban ya ce, “Mun yi wannan huɓɓasa ne, domin mu nunawa Gwamnati cewar, tabbas mun san akwai wadaccen arziƙin da za a iya ɗaukar nauyin kula da Ilimi.
“Iyaye basa iya bamu goyon baya, a duk lokacin da mu ka yo yunƙurin ganin an haɗa hannu domin kawo gyara, kawai sai su tsaya su zuba mana idanu. Muna son Iyaye su sani, mu ba wani abu mu ke buƙata daga gare su ba, kawai so mu ke su haɗa hannu damu, su goya mana baya a gwagwarmayar da mu ke cigaba da yi, dan ganin mun inganta goben Ilimi, da ƴaƴayennmu”.