Labarai

Tallafin Mai : An Umarci Ƴan Jarida Su Tsunduma Yajin Aiki

Ƙungiyar Ƴan Jaridu ta ƙasa (NUJ), ta umarci membobinta da su shiga yajin aikin da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar nan (NLC) ta ƙuduri aniyar shiga, domin nuna rashin amincewarta da matakin da Gwamnatin tarayya ta ɗauka, na cire tallafin man_fetur.

NUJ, ta bayyana hakan ne dai, ta cikin wata sanarwar manema labarai da ta fitar, a babban birnin tarayya Abuja, wacce ke ɗauke da sa hannun Sakataren yaɗa labaranta, Shuaibu Usman Leman, Inda sanarwar tace Kwamitin gudanarwar ƙungiyar ya yi wa lamarin duba na tsanaki, tare da fahimtar cewar matsayar da ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ke kai ita ce dai-dai, kuma ita ta dace da buƙatun al’ummar Najeriya.

Ta na mai cewar, ”Bayan gabatar da buƙatar tattaunawa kan wannan mataki da NLC ke shirin ɗauka, da Shugaban ƙungiya na ƙasa, Chris Isiguzo, tare da Ma’aji, Bamidele Atunbi su ka yi, membobin kwamitin gudanarwar wannan ƙungiya, sun amince da bin matsayar NLC, kan wannan batu.

”Kwamitin zartarwa ya aminta da cewar, cire tallafin man abu ne da zai taimaka matuƙa wajen cigaban ƙasa, da ma samar da ƙarin ayyukan yi, Sai dai cire shi kuma, da aka yi a yanzu babu zato ba tsammani abu ne da ka iya kaiwa ga haifar da matsalolin zamantakewa, dan haka akwai buƙatar ɗaukar dukkannin mataki, na tilastawa gwamnati, wajen ganin ta janye wannan mataki na ta, tun daga kan zanga-zanga, zuwa Yajin Aiki.

”Kwamitin gudanarwar ya kuma lura da yadda tun a baya daman farashin ya tashi, wanda hakan ya haifar da tashin gwauron zabin farashin kayayyaki, da ma yawan adadin man da jama’ar ƙasa su ke iya saya.”

”Saboda haka, kwamitin zartarwar na umartar dukkannin rassan wannan ƙungiya na jihohi da su tattara membobinsu, tare da fara gudanar da zanga-zanga, a faɗin ƙasar nan, daga ranar Larabar mako mai kamawa, 7 ga watan Yunin 2023, muddin dai kamfanin mai na ƙasa, bai janye matakin ƙara farashin man da ya ɗauka ba”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button