Labarai

Tallafin Mai : Za a Yi Fama Da Duhu A Ƙasar Nan, Bayan Da Ma’aikatan Lantarki Su Ka Amince Da Tsunduma Yajin Aiki A Ranar Laraba

Akwai yiwuwar fama da duƙununun duhu a faɗin ƙasar nan, bayan da ma’aikatan wutar lantarki su ka bayyana aniyarsu ta yin biyayya ga ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), wajen tsunduma Yajin Aiki, tare da gudanar da zanga-zanga, daga ranar Laraba, 7 ga watan Yunin da muke ciki, domin nuna rashin amincewarsu ga matakin da Gwamnatin tarayya, ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu, ta ɗauka, na cire tallafin man fetur, wanda hakan ya jawo tashin farashinsa, a ƙasar nan.

Ƙungiyar ma’aikatan lantarki ta ƙasa ce dai, ta bayyana wannan aniya ta ta, ta cikin wata sanarwa da ta fitar, mai ɗauke da kwanan watan 2 ga watan Yuni, wacce kuma ke ɗauke da sa hannun babban Sakataren ƙungiyar, Dominic Igwebike.

”Biyo bayan taron gaggawa da majalissar zartarwar ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta gudanar, a ranar 2 ga watan Yunin 2023, a ofishin ƙungiyar da ke Abuja, kan batun cire tallafin mai da Gwamnatin tarayya ta yi bagatatan, wanda hakan kuma ya jefa rayuwar da dama daga cikin jama’ar Najeriya a cikin ƙunci, tare da haifar da tashin farashin kayayyakin masarufi, NLC ta umarci da a tsunduma Yajin Aiki, daga ranar Laraba, 7 ga watan Yunin 2023”, a cewar sanarwar.

Ƙudurin tsunduma Yajin Aikin kuma, na nuni da cewar, za a samu rashin wuta, a ƙasar nan, daga 12:00 na daren Laraba.

”Muna sanar da ku cewar, za mu dakatar da gudanar da Aikinmu ne, daga sa’a ta 0.00 na Laraba, 7 ga watan Yunin 2023”, a cewar sanarwar.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button