Tarihin Barista Saidu Tudunwada, Sabon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyi Musulmai Ta Ƙasa
An haifi Barista Saidu Muhammad Tudunwada, LL.B, BL, LL.M, LL.D (bai kammala ba), ACIARB ne, a ranar 17 ga watan Afrilun 1969.
Ya yi karatun Digirinsa na farko, a fannin shari’a, a Jami’ar Bayero, da ke birnin Kano, inda ya samu nasarar kammalawa a shekarar 1994, Sannan ya ɗora da karatun Digirinsa na biyu (Master’s), a fannin nazarin shari’a na Jami’ar ta Bayero, inda ya samu shaidar ƙwarewa a fannin dokokin Kamfanoni. Ya kuma samu horo a mabanbanta a ɓangarori daban-daban na fannin na shari’a.
Ya kuma fafata a shari’u mabanbanta, a ciki da wajen ƙasar nan, a wasu lokutan ya wakilci mutane, a wasu lokutan kuma ya wakilci ƙasa.
Ya tsayawa Hukumar Samar Da Katin Ɗan Ƙasa (NIMC), Hukumar Zaɓe (INEC), Majalissar Wakilai Ta Ƙasa (National Assembly), da Bankunan Kasuwanci da dama, gami da masana’antu masu zaman kansu iri-iri, a shari’u mabanbanta.
Ya yi shari’u a gaban Manyan Kotunan Tarayya da na Jihohi, Kotun Ɗaukaka Ƙara, har ma da Kotun Ƙoli.
Ya kuma gabatar da muƙalu da dama, a taruka mabanbanta.
Ya yi Aiki da tarin kwamitoci, da ƙungiyoyin fannin shari’a, cikinsu har da ƙungiyar Lauyoyi ta Nigerian Bar Association (NBA).
Barista Tudunwada, ya shafe tsawon shekaru ya na aiki da ƙungiyar Lauyoyi Musulmai ta MULAN, inda ya riƙe muƙamin mataimakin shugabanta na jihar Kano, na biyu, a tsakanin 2018 zuwa 2020.
Daga baya, ya zama Mataimakin shugaban ƙungiyar ta MULAN na ƙasa (na 2), a tsakanin 2020 zuwa 2022, lokacin Shugabancin Farfesa Abdulkadir Ibrahim Abikan.
Ko a yanzu ma kuma, Barista Saidu Muhammad Tudunwada ɗin, shi ne ke riƙe da muƙamin mataimakin shugaban MULAN ɗin na ƙasa (na farko), ƙarƙashin Shugabancin Dr. Kazeem Olaniyan.
A gefe guda kuma, yanzu haka shi ne shugaban Kwamitin Kuɗi, na ƙungiyar Lauyoyi ta NBA, reshen jihar Kano.
A yanzu haka, ya na karatun Digirinsa na uku (LL.D), a Jami’ar Jos, da ke jihar Plateau.
Ya Auri Barista Fatima Babadisa Goji, kuma sun azurta da haifar yay ra bakwai.