Tarihin Rayuwar Jarumi Adam Garba (Raba-Gardama)
Cikakken sunan Jarumin shi ne, Adam Garba, kuma an haife shi ne a Jos, inda ya yi karatunsa na Firamare da na Sakandire a can.
Bayan kammala Sakandire ne kuma, sai ya wuce zuwa Jami’ar Jihar Nasarawa (Nasarawa State University), Keffi, inda ya yi Digirinsa na Farko akan harkar Banki Da Sarrafa Kuɗaɗe (Banking & Finance), ba ya ga haka kuma ya yi kwasa-kwasai kan Rubutun Film (Scriptwriting), Taka rawa a matsayin Jarumi (Acting), inda tun ya na Sakandire ya ke a ƙungiyar Drama ta Makaranta.
Ya kuma kasance mai sha’awar zama Jarumi, tun ya na shekaru 4 zuwa 5 a duniya, inda ya kan gwada wasan kwaikwayo, irinsu: kukan ƙarya.
Sai dai duk da wannan sha’awa tasa, rashin sanin wani a masana’antun shirya fina-finan Arewaci da na Kudanci ya zamewa wannan sha’awa da basira tasa ciwon ido, domin kuwa ba shi da mai saka shi a Film.
Sai a wani lokaci ƙaninsa ya ce masa, ana Audition ɗin wani Film na Nollywood ya je ya gwada, kuma bayan ya je sai ya haɗu da, Robert Peters wanda ya zo daga Ingila, ya kuma tantance, sannan ya bashi Role, a cikin shirin ‘Voiceless’.
Bayan fitar shirin ne kuma, sai ya yi suna da tashe, wanda hakan ya sanya a shekarar 2018, Daraktan shirin Kwana Casa’in, Salisu T. Balarabe, ya kira shi, tare da bayyana masa cewar, ya ga wasu ƙananan Ayyukansa a YouTube, kuma yana son ya je ya taka masa rawa a wani Film ɗinsa mai suna Kwana Casa’in, na tashar Arewa24, Kano.
Daga Kwana Casa’in kuma, bai sake shiga cikin wani shirin Hausa ba, sai ‘Labarina’ na Darakta Aminu Saira, inda ya fito a matsayin Raba Gardama.
Abin koyinsa (Mentor) a harkar Film shi ne, Sani Mu’azu.
Kuma ba shi da Aure, sai dai ya na sa ran yi, a nan kusa.