Tarwatsa Masu Zanga-Zanga, Ya Gagari Ƴan Sanda A Birnin Kano
Wasu gungun masu zanga-zanga sun fantsama kan tituna a ƙwaryar birnin Kano, domin nuna fushinsu kan hukuncin tsige Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, na jam’iyyar NNPP, da Kotun ɗaukaka ƙara ta yi.
Idan ba a manta ba dai, a makonni biyu da suka gabata ne, kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hukuncin kotun sauraron ƙarar zaɓen Gwamnan jihar, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a, Oluyemi Akintan Osadebay, wanda ya tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf ɗin daga kan kujerarsa, tun a ranar 20 ga watan Satumban shekarar da mu ke ciki.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen dai, ta soke nasarar Abba ne, bayan da ta bayyana cewar ƙuri’u 165,000 daga cikin waɗanda Gwamna Abba Kabir Yusuf din ya lashe zaɓe da su, a matsayin na boge, sakamakon rashin sanya hannu da sitamfin jamián hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).
Hakan ne ya sanya ƙuri’un Gwamnan su ka ragu zuwa 853,939, ya yin da Nasiru Yusuf Gawuna, na jam’iyyar APC wanda ke a matsayin Abokin takararsa ya ke da ƙuri’u 890,705, hakan ne kuma ya sanya Kotun ta ayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.
Sai dai, Abba Kabir Yusuf, ya yi watsi da hukuncin wanda ya bayyana a matsayin rashin Adalci, tare da garzayawa gaban Kotun Ɗaukaka Ƙara, da ke babban birnin tarayya Abuja, domin ƙalubalantar hukuncin.
Sai dai, a Kotun Ɗaukaka Ƙarar ma lamarin bai sauya zani ba, domin kuwa Kotun ta ƙara soke nasarar Abba, bisa hujjar rashin kasancewarsa ɗan jam’iyya, wanda hakan ne ya sanya Magoya baya da ƙungiyoyi da dama gudanar da zanga-zangar lumana, domin nuna fushinsu kan lamarin.
Ko a ranar Litinin ma, sai da wasu gungun mutane su ka fara gudanar da zanga-zangar, kafin Jami’an Ƴan Sanda su tarwatsa su.
Sai dai, kwanaki biyu bayan aukuwar hakan, sai ga masu zanga-zangar sun ƙara fitowa kan tituna, ɗauke da kwalayen da aka rubuta, ,”Ba Zamu Amince Ba”; “Ba Zamu Lamunta Ba”; “Kano Ta Abba Ce”; “Wajibi Ne A Dawo Mana Da Abin Da Mu Ke So”; “An Tafka Rashin Adalci A Kotun Ɗaukaka Ƙara “, da makamantansu.
Jami’an tsaro, sun kuma yi yunƙurin tarwatsa masu zanga-zangar, sai dai lamarin ya ci tura, bayan da su ka ding tarwatsewa, su na kuma sake dawowa su haɗe.
Idan ba a manta ba dai, rundunar ƴan sandan jihar ta Kano, ta gargaɗi al’umma kan gujewa dukkannin wani nau’i na zanga-zanga, musamman ma wacce ke da alaƙa da hukuncin Kotun ɗaukaka ƙara.