Tattalin Arziƙin Najeriya Na Cigaba Da Fuskantar Koma Baya
Har yanzu tattalin Arzikin Najeriya bai dawo hayyacinsa kamar yadda aka yi tsammani ba, tun bayan fuskantar barkewar annobar Covid-19, wacce ta haifar da gagarumar hauhawar farashin kayayyaki, wanda ya shafi fannin mai da iskar gas, da su ma ake fuskantar karancin fitar da su. Jawabin hakan ya fito ne ta bakin, Shugaban sashen lura da tattalin Arziki, Oyindamola Adeyemi, a ya yin da ya ke batu kan tsarin tattalin arzikin da duniya ke fuskanta na shekarar 2023.
A cikin jawabin nasa dai, Adeyemi ya ce, har yanzu tattalin arzikin kasar nan ya na cigaba da kasancewa a baya ta fuskar habbaka, tun bayan annobar da aka fuskanta, ba kamar yadda aka tsammata ba.
Sai dai ya bukaci, kasar nan da ta kaddamar da tsare-tsaren kasuwanci na zamani, dan ganin ta daga likkafar alámuran kasuwanci, da nufin bunkasa tattalin arzikin kasa, a karkashin gwamnatin da ke tafe.
Ya kuma bayyana gamsuwarsa kan yiwuwar bunkasar tattalin arzikin kasar nan bayan rantsar da sabuwar gwamnati a ranar 29 ga watan Mayun da mu ke ciki, muddin sabuwar gwamnatin ta dauki matakan da su ka dace.