Kasuwanci

TCN Ya Yi Asarar Injinan Taransifoma Na Sama Da Dala Miliyan 4, A Kebbi

Ma’aikatan kamfanin samar da wutar Lantarki na ƙasa, TCN, su na Aiki ba dare – ba rana, wajen ganin an dawo da samar da wuta a jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara, biyo bayan ɓarkewar gobarar da aka samu, a Cibiyar wutar lantarki ta Birnin Kebbi, a daren Alhamis.

Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa NAN, ya rawaito cewar, wasu Injinan Sarrafa wutar lantarki na taransifoma masu 90MVA (330KV/132KV) da 60MVA (132KV/33KV) sun lalace, sakamakon tashin gobarar, waɗanda kimarsu ta kai, Dalar Amurka miliyan 4.

Da ya ke zantawa da Manema Labarai, a Birnin Kebbi, bayan duba irin ɓarnar da gobarar ta yi, a ranar Alhamis, Daraktan Gudanarwa kuma Shugaban Kamfanin na TCN, Sule AbdulAzeez, ya bayyana ɓarnar a matsayin gagaruma.

AbdulAzeez ɗin ya kuma ce, domin samar da gyara mai inganci, zai ɗauki kamfanin tsawon makonni biyu, kafin kammala gyara taransifomomin da ma dawo da bayar da wutar lantarki, a yankunan da abin ya shafa.

Ya kuma roƙi Kwastomominsu da su yi haƙuri, sakamakon abin ya faru ne, ba tare da tsammani ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button