Ilimi

TETFund Ta Ƙaddamar Da Ayyukan Sama Da Biliyan 2, A FCE-T Bichi

A ranar Talata ne, Asusun tallafawa manyan makarantu na kasa TETFund, ya kaddamar da ayyukan da su ka lakume Naira biliyan 2.1, a Kwalejin Ilimi ta tarayya da ke garin Bichi, a jihar Kano. Babban Sakataren Asusun, Mr Sonny Echono, wanda ya gabatar da jawabi a ya yin bude ayyukan, ya ce an samar da ayyukan ne bisa tsarin gudanar da ayyuka na shekarun 2015, 2016, 2017 da ma 2019. A cewar sa dai, ayyukan sun hadar da dakunan daukar darasi, ofisoshi, kayayyakin amfani da makamantansu.

Sakataren, wanda ya samu wakilcin daraktar Asusun ta shiyyar Arewa maso yamma, Bilkisu Zangon-Daura, ya ce, Gwamnatin tarayya na yin dukkannin mai yiwuwa wajen ganin ta inganta alámuran koyo da koyarwa a kasar nan, ta hanyar sanya hannun jari, a karkashin wannan asusu. Shugaban na Tetfund ya kuma kara da cewar, An samar da Naúrori masu kwakwalwa na koyarwa, kayayyakinb amfanin yau da kullum, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, litattafai da sauran kayayyakin karatu da kimarsu ta kai Naira biliyan 1, a makarantar.

A nasa bangaren, Shugaban Kwalejin ce wa ya yi, a yanzu makarantar tasu ta samu karin ajujuwan karatu kimanin 58, Dakunan daukar darasi da gudanar da taruka kimanin 18, Ofisoshi 125, Bandakuna 172, wanda hakan ba karamin cigaba bane ga kwalejin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button