Tinubu Na Ɗaga Likkafar Najeriya Zuwa Mataki Na Gaba – Ganduje
Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya buƙaci al’ummar Najeriya da su kasance masu haƙuri, akan matakan da Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ke cigaba da bijiro da su, ya na mai cewa, Tinubun na ɗaukar waɗan nan matakai ne, domin sake gina tattalin arziƙin Najeriya, bayan gurgunta shi da aka yi na tsawon shekaru, da ma guragun matakan da gwamnatocin baya su ka dinga ɗauka.
Ganduje, yayi wannan iƙirari ne, ranar Litinin, yayin da ya karɓi baƙuncin shuwagabannin masu buƙata ta musamman, na Jihohi 36 da ke tarayyar Najeriya, a Sakatariyar jam’iyyar APC, da ke babban birnin tarayya Abuja.
Wakilan masu buƙata ta musamman ɗin, waɗanda suka kai wa shugaban ziyarar girmamawa, tare da sake jaddada matsayarsu ta goyon bayan shugaban APC ɗin na ƙasa, sun bayyana irin ƙwarin guiwar da su ke da shi akan shugabancinsa.
Da ya ke gode musu, kan yaba ƙoƙarinsa da suka yi, Ganduje ya roƙi al’ummar Najeriya da su kasance masu haƙuri akan matakan da Gwamnatin Tinubu ta ke cigaba da ɗauka, ya na mai cewar, babu shakka tsare-tsaren nasa za su kai Najeriya zuwa mataki na gaba.
A nasa jawabin tun da fari, shugaban masu buƙata ta musamman na jam’iyyar APC, Tolu Bankole, ya koka kan yadda shuwagabannin Siyasa suke mantawa da gudunmawarsu, ba tare da duba su ba, idan aka kai gaci.