Tinubu Na Shirin Yaƙar Yunwa Ta Hanyar Kimiyya – Minista
Ministan Kimiyya da Fasaha, Uche Nnaji, ya bayyana cewar, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na shirin yaƙar yunwa, ta hanyar amfani da Kimiyya da Fasaha.
Ministan, ya bayyana haka ne, yayin da ya ke gabatar da jawabin buɗe Taron Ƙungiyar Malaman Kimiyya Na Yammacin Afirka, reshen Najeriya (WANNAS), ranar Talata, a babban birnin tarayya Abuja.
“Ina mai farincikin sanar da ku cewar, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya mayar da hankali matuƙa kan yaƙar yunwa da fatara, ta hanyar amfani da Kimiyya da Fasaha.
“Haka zalika, hukumarmu na yin dukkannin mai yiwuwa wajen bunƙasa wannan ilimi na fasaha a ƙasar nan, ta hanyar ɓullo da sababbin shirye-shirye, domin samar da ayyuka, da bunƙasa tattalin arziƙi”, a cewarsa.
Ministan, ya kuma bayyana cewar, babu tarihin ƙasar da ya ke cika ta fuskar kima, ba tare da ta mayar da hankali kan bunƙasa Kimiyya da Fasaha ba.