Ilimi

Tinubu Ya Dakatar Da Shirin Cire Kaso 40 Na Harajin Jami’o’i

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya soke shirin fara cire kaso 40 na kuɗaɗen harajin cikin gida (IGR) da Jami’o’in ƙasar nan su ke tarawa, bayan da ya ce ko kaɗan shirin bai dace da wannan lokacin ba.

Tinubu, wanda ya samu wakilcin Ministan Ilimi, Tahir Mamman, ya bayyana hakan ne ranar Juma’a, a ya yin bikin ranar Founder’s Day, karo na 75, da ke cigaba da gudana, a Jami’ar Ibadan (UI).

Da ya ke gabatar da jawabi a Jami’ar, Tinubu ya yi alƙawarin mayar da hankali kan farfaɗo da harkar Ilimi, domin bunƙasa cigaban ƙasa.

“An soke tsarin cire kaso 40 kaitsaye daga kuɗaɗen harajin Jami’o’in ƙasar nan. Ba yanzu ne lokacin da ya dace a aiwatar da wannan shirin ba, duba da yadda Jami’o’inmu su ke cikin gwagwarmaya da fafutukar ƙaƙanikayi”., a cewar Tinubu.

A jawabinsa na Maraba, tunda fari, Uban Jami’ar ta Ibadan, kuma Sarkin Sokoto, Sa’adu Abubakar, ya yi tir! da tsarin, bayan da ya hakaito halin ƙalubalen da Jami’o’in ƙasar nan ke fuskanta.

Abubakar, ya kuma roƙi hukumomin da abin ya shafa, da su yi watsi da shirin, ya na mai bayyana cewar tsarin zai kawo koma baya ga tsarin tafiyar da Jami’o’i.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button