Labarai
Tinubu Ya Gana Da Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
A ranar Lahadi, 3 ga watan Disamba ne, shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gana da shugaban haɗaɗɗiyar daular Larabawa, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan.
An kuma gudanar da ganawar ne, da nufin sake ƙarfafa kyakykyawar dangatakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamman, kan kafafen sada zumunta na zamani, Dada Olusegun, shi ne ya wallafa hotunan ganawar tasu, ta shafinsa na kafar sada zumunta ta X.
Inda ya wallafa cewar, “Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya samu ganawa da shugaban haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, Sheikh Mohammed bin Zayed Al Nahyan a yau, tattaunawar ta mayar da hankali ne, is yadda za a sake inganta alaƙa da hulɗoɗin da ke tsakanin ƙasashen biyu”.