Tinubu Ya Naɗa Sabon Gwamnan CBN
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin, Dr. Olayemi Michael Cardoso, a matsayin sabon Gwamnan Babban Bankin Ƙasa (CBN), inda zai shafe tsawon shekaru biyar akan wannan muƙami a zangon farko, da zarar Majalissar Dattijai ta tabbatar da shi.
Bayanin naɗin nasa kuma, na ɗauke ne, ta cikin wata sanarwa da Mai Bawa Shugaban ƙasa shawara na musamman kan yaɗa labarai, Chief Ngelale, ya fitar, da yammacin ranar Juma’a.
“Wannan naɗi kuma ya yi dai-dai da tanadin sashe na 8 (1) na dokar Babban Bankin Ƙasa ta shekarar 2007, wacce ta bawa Shugaban ƙasar Najeriya ikon naɗa Gwamnan na CBN, da Mataimakansa guda huɗu, bisa amincewar Majalissar Dattijai”, a cewar jawabin.
“Bugu da ƙari, Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin mataimakan Gwamnan guda 4, waɗanda su ma za su shafe tsawon shekaru biyar-biyar a zangon farko, idan Sanatoci sun amince da su, Ga sunayensu a ƙasa:
(1) Mrs. Emem Nana Usoro
(2) Mr. Muhammad Sani Abdullahi Dattijo
(3) Mr. Philip Ikeazor
(4) Dr. Bala M. Bello
A sababbin tsare-tsaren da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ke cigaba da ɓullowa da su, ya na fatan waɗannan mutane da aka lissafa a sama, za su tsamo Babban Bankin na ƙasa, daga halin ƙamshin mutuwar da ya tsinci kansa, Wanda zai ƙarawa Jama’ar ƙasa da ma Abokanan hulɗa na ƙasashen waje ƙwarin guiwa kan sake farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya.