Kasuwanci

Tinubu Zai Ƙaddamar Da Ginin Gidaje 3,112 A Karsana

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, zai kaddamar da ginin gidaje 3,112, da gwamnati za ta samar, a yankin Karsana, da ke babban birnin tarayya Abuja.

Kaddamar da aikin, wanda aka tsara gudanarwa ranar Alhamis, wani bangarene na aikin hadaka tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu, da aka rattaba hannu akansa cikin watan Disambar 2023, tsakanin maáikatar gidaje ta tarayya, da wasu rukunin kamfanoni, da su ka hadarda kamfanin Continental and General Construction Limited, da Ceezli Limited, inda aka tsara samar da gidaje dubu 100, a fadin kasar nan.

Wani jawabi, da maáikatar samar da gidaje da kawata birane ta tarayya ta fitar, ya bayyana cewar, za a samar da rukunin gidaje dubu 20 da ke cikin yarjejeniyar ne a babban birnin tarayya Abuja, inda guda 3,112 daga cikinsu, za su kasance a yankin Karsana.

Za kuma a samar da dukkannin gidajen ne a biranen kasar nan, domin bunkasa samuwar muhallai ga alúmmar kasa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button