Tinubu Zai Gana Da Zaɓaɓɓun Ƴan Majalissun Adawa, A Yau
Ana sa ran zaɓaɓɓun Sanatoci, da Ƴan Majalissun Wakilan adawa, da su ka fito daga jam’iyyun PDP, LP, NNPP, da sauran jam’iyyun adawa, za su gana da Shugaban ƙasa, a yau (Litinin).
Za kuma a gudanar da taron ne daban-daban, inda na ƴan majalissar wakilai, zai kasance a Fadar Gwamnatin tarayya, da ke Abuja, da misalin ƙarfe 5 ɗin yammacin yau.
Takardar gayyatar da shugaban ƙasar, ya yi wa zaɓaɓɓun ƴan majalissun zuwa ganawar kuma, na ɗauke ne da sa hannun Babban Sakataren Majalissar, Tijani Umar.
Inda su kuwa Sanatocin tsagin adawa, za su gana da Shugaban ƙasar ne, da misalin ƙarfe 3, na yammaci.
Ana kuma sa ran tattaunawar tasu za ta mayar da hankali ne, kan samar da shugabancin majalissar ta 10.
Wa’adin majalissar tarayya ta tara dai, zai kawo ƙarshe ne a ranar 13 ga watan Yunin da mu ke ciki, ya yin da ake sa ran rantsar da sabuwar majalissa a wannan makon.