Tsaigumi: An Gano Wani Makeken Wurin Ajiya Da Ake Jibge Kayan Tallafin Abincin Gwamnatin Kano, Da Aka Sace
Rahotanni, sun tabbatar da yadda aka gano wata ma’ajiya da ake ɓoye kayayyakin tallafin Abincin da Gwamnatin Kano ke rabawa al’umma, wanda aka sata.
Kwamishinan harkokin noma na jihar Kano, Dr. Danjuma Mahmud shi ne ya bayyana yadda aka gano wurin, ya yin da ya ke zantawa da Manema Labarai, da yammacin yau (Asabar), jim kaɗan bayan da tawagar Gwamnan Kano ta kai ziyara wurin.
Tuni dai, aka cika hannu da mutanen da ake zargi da wannan aika-aika da ke kama da zamba cikin aminci, ta hanyar sace kayayyakin da ake rabawa al’umma kyauta domin rage raɗaɗi.
Mutanen da ake zargin, su na sauyawa kayayakin Abincin buhunhuna ne, kafin daga bisani su cefanar da su.
A zantawar Kwamishinan da manema labarai, ya ce za a faɗaɗa bincike domin gano sauran mutanen da ke cikin wannan almundahana, dan ganin sun fuskanci hukunci.