Tsaigumi

Tsaigumi: An Hangi Ganduje Yana Sharara Barci, A Ya Yin Yanke Hukuncin Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa

Cikin wata ɗaukar kaitsaye da kafar Talabijin ta Channels ta haska, daga farfajiyar Kotun Sauraron Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa, wacce ke yanke hukunce-hukuncenta, a yau (Laraba), an hangi Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, da Gwamnan Bauchi, Bala Muhammad Ƙaura, tare da wasu masu ruwa da tsaki, Lauyoyi, har ma da Ƴan Jaridu su na sharara barci, a ya yin da Kotun ke karanta hukunce-hukunce kan ƙararraki mabanbanta da ƴan takarkarun jam’iyyun adawa su ka shigar, su na ƙalubalantar nasarar Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Har ya zuwa yanzu kuma, babu wani sahihin zance, da ke bayyana takamaiman dalilin yin wannan barci. Sai dai, dama tun a baya, ana ganin tsohon Gwamnan na Kano, a matsayin mai yawan yin barci, a ya yin tarurruka mabanbanta.

Kotun, ƙarƙashin Jagorancin Mai Shari’a, Haruna Tsammani, ta kori dukkannin ƙararrakin da jam’iyyar APM ta shigar, tare da na ɗan takarar Labour Party, Peter Obi, Inda a halin yanzu kuma ta ke tsaka da zartar da hukunci kan ƙararrakin da Atiku Abubakar, na Jam’iyyar PDP, ya shigar gabanta.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button