Tsaigumi

Tsaigumi: Yadda Aka Ɗaurawa Yarinya Mai Shekaru 12 Aure A Kano

Aure Sunnah ce ta Ma’aiki Sallallahu Alaihi Wasallam, babu musu kuma kan cewar, Annabi ya Auri Sayyadata Aisha tana da shekaru 9 a duniya. Sai dai Ma’aiki ya raineta ne, har zuwa lokacin da ta zama Cikakkiyar mace kafin gabatar da mu’amalar Aure da ita.

Dalilin wannan shimfiɗa da mu ka gabatar kuwa, ba ya rasa nasaba da wani labari mai ban tausayi da al’ajabi, da Jaridar Rariya Online ta zaƙulo muku, inda aka ɗaura Auren wata yarinya mai shekaru 12 kacal a duniya.

Wannan lamari dai, ya faru ne, unguwar Bachirawa, da ke ƙaramar hukumar Ungogo, a birnin Kanon Dabo, inda aka Aurar da wata yarinya mai suna Shamsiyya, makonni biyu da su ka gabata.

Wannan batu kuma na ƙunshe ne, ta cikin wani rubutu da ƴar uwa ga Maƙobciyar wacce lamarin ya faru da ita, mai suna, Nusaiba Shafiu, ta wallafa da safiyar yau (Asabar) a shafinta na Facebook.

Babban abin tsoron kuma, shi ne yadda tuni yarinyar ta tare a gidan mijinta, tun makonni biyu da su ka gabata, wanda hakan ke hakaito da yiwuwar Mijin da ya Aureta ya kusanceta, mun kuma kwana da sanin yadda haikewa yara masu ƙananun shekaru kamar Shamiyyan ke jawo musu ciwon yoyon fitsari, ya yin haihuwa (idan aka samu akasi).

Ga kuma tauye mata damarta ta samun ingantaccen Ilimi da za mu iya cewa an yi, ba ya ga jefa rayuwarta cikin garari (ku yi wa wannan batu kallo ta fuskar fahimta).

Ga abin da matashiyar ta wallafa, shafinta na Facebook: “Nasha mamaki danaga hotunan bikin yarinyar nan 🤔🤔.

“Banace haramun bane Manzon Allah ya auri Nana A’isha tanada qananun shekaru yayi rainonta …

“Kusa da gidan qanwata wlh ita take aike kai caji 😩😩 Wai ranar naga tayi posting anyi bikin shamsiya nasha mamaki har ena daukar abun shirme yarinya dai tana dakinta 2weeks kenan dayin bikin Acikin Kano fa a bachirawa 😢😢

“Yanxu fisabilillahi yarinyarda bata wuce 12years ba me ta sani akan aure ? Ba’a fatan matsala amma irin Hakane yara suke kamuwa da matsalar yoyon fitsari …

“Idan anyi Sa’a ta iya karanta hizib 2 anya tasan hukunce hukuncen tsarki ma kuwa ?? Ya Allah

“Annabi ya raini Nana A’isha harta zama mace amma wannan yarinyar shi wanda aka kaima ita ko shekarar sa 50 zai iya paɗa mata 🥺🥺 sbd anayima yara qanana fyade ma… Amma wannan magana ake ta aure…

“Manyan ma yanxu ana fama dasu ta fannin ilimi balle wannan Abar… Allah yasa mugama lpy”, a cewarta.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button