Tsohon Ɗan Takarar Shugabancin APC Ya Buƙaci Kotu Ta Sauke Ganduje Daga Muƙaminsa
Tsohon Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar APC na ƙasa, Mohammed Saidu-Etsu, ya shigar da ƙara a gaban Kotu, ya na buƙatar ta soke naɗin da Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar na Ƙasa ya yi wa, Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin shugaban jam’iyyar ta APC.
Ta cikin ƙunshin ƙarar, wacce ya shigar a gaban Babbar Kotun Babban Birnin Tarayya Abuja, a ranar Juma’a, Etsu ya buƙaci Kotun da ta ayyana naɗin a matsayin wanda ba ya kan doka, kuma ya saɓawa kundin tsarin dokoki, dan haka babu shi kwata-kwata.
Ya kuma ƙara da buƙatar Kotun ta bada umarnin haramtawa Ganduje kiran kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, ta kowacce fuska.
Bugu da ƙari, ya buƙaci Kotun da ta soke dukkannin wasu matakai da Gandujen ya zartar, tun bayan ɗarewarsa kan karagar shugabancin jam’iyyar a ranar 3 ga watan Augustan 2023.
Mai ƙarar ya ce, a kundin tsarin dokokin jam’iyyar, ana ayyana mutum a matsayin shugabanta ne kawai, ta hanyar zaɓe.
Ta cikin ƙunshin ƙarar, wacce ya shigar ta hannun Lauyoyinsa, J. Obono-Obla da M.M. Aggrey, mai ƙarar ya buƙaci Kotun da ta fassara ko naɗin na Abdullahi Umar Ganduje, wanda ɗan yankin Arewa Maso Yamma ne, da Kwamitin Zartarwar Jam’iyyar ya yi, a ranar 3 ga watan Augustan 2023, ya dace da “sashe na 14.2[ii] na dokokin jam’iyyar ?”, bayan ajiye muƙamin da Sanata Abdullahi Adamu ya yi.