Tsotsar Yatsa Zai Iya Haifar Da Fashewar Haƙora – Masana Lafiya
Fitaccen Likitan Haƙora, da ke aiki da Asibitin Jami’ar Ibadan, Dr Zakka Baraya, ya bayyana cewar, tsotsar yatsa zai iya haifar da fashewar haƙora, tare da samar da faffaɗar tazara a tsakaninsu.
Baraya, wanda ke zama Babban Magatakardan sashen kula da lafiya haƙora na Asibitin UCH Ibadan, ya bayyana hakan ne, ranar Talata, ya yin ganawarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa (NAN), a Ibadan.
Ya kuma ce, tsotsar yatsar ga ƙananun yara, abune da zai sanya faɗin dadashinsu ya ƙaru, tare da sauya musu fasali baki ɗaya.
“Shan Yatsa zai iya haifar da Matsaloli wajen furta magana, ba ya ga yiwuwar hana baki fahimtar dukkannin wani abu da ke taɓa shi”, a cewarsa.
Ya kuma ce, yatsar da ake sawa a bakin akwai yiwuwar tana ɗauke da ƙwayoyin cutar bacteria, da datti, wanda shigar da ita bakin zai basu damar shiga cikin jikin mutum, baya ga gurɓata masa yawu.
“Yatsar da ake sakawa a bakin kuma, za ta iya jawo tsagewar fatar harshe, zubar da jini, har ma ta kan iya zama gagarumin ciwo”, a cewarsa.
Tsotsar yatsa dai, wata ɗabi’a ce da ake gani a wurin yara da dama, da ke ƙasa da shekaru huɗu, inda kuma mafi yawa su kan dakatar da wannan ɗabi’a da zarar sun girma.
Sai dai, a wasu lokutan, akan samu manyan da ake girma, ba tare da sun jefar da wannan ɗabi’a ba.