Zamantakewa

Uba Ya Hallaka Jaririyarsa A Kano, Bayan Haifa Masa Mace A Madadin Namiji

Ana zargin wani mutum mai shekaru 28 a duniya, Musbahu Salisu, da laifin hallaka Jaririyarsa mai kwana guda a duniya, sakamakon fin son haifar ɗa namiji, da ya yi.

Kuma tuni rundunar Hisbah ta jihar, ta samu nasarar daƙume mutumin, wanda ke zaune a ƙauyen Doka Baici, a yankin ƙaramar hukumar Tofa, ta jihar Kano, a ranar Juma’a.

Hukumar kuma, ta bayyana cika hannunta da mutumin ne, ta cikin wata sanarwa da Mataimakin Kwamanda Janar na rundunar, Mujahid Aminudeen ya fitar.

Aminudeen ya ce, mutumin ya bayyana musu cewar, ya yi amfani da maganin kashe ƙwari na Fiya-Fiya ne wajen hallaka ƴar tasa.

“Salisu ya kuma bawa Mahaifiyar Jaririyar mai suna, Sa’ade, kofin shayi da ke ɗauke da maganin barci, a ya yin da ya ke shirin aikata wannan ta’asa.

“Wanda ake zargin kuma, ya amince da aikata laifinsa, inda ya ce yafi son jariri Namiji ne, amma Matarsa ta haifar masa Mace, wanda hakan ya hassala shi, har ya ɗauki Matakin hallaka jaririyar”, a cewar jawabin.

Mataimakin Kwamandan ya kuma ce, sun miƙa mai laifin zuwa ga rundunar ƴan sandan jihar, domin faɗaɗa bincike, da ma gurfanar da shi a gaban Kuliya.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button