Siyasa

Ubangiji Zai Kare Sababbin Masarautun Kano – Martanin Ganduje

Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewar, zai cigaba da roƙon Ubangiji da ya kare sababbin Masarautun jihar, waɗanda gwamnatinsa ta samar, daga dukkannin masu nufinsu da sharri.

Inda Gwamnan ya ce, sababbin Masarautun za su cigaba da kasancewa har Illa-Masha’Allah!.

”Ko da ba ma Gwamnati, muna Addu’a, tare da cigaba da roƙon Ubangiji da ya kare waɗannan Masarautu, daga maƙiya. Na gode muku”, a cewar Ganduje.

Gwamnan mai barin gado, ya bayyana hakane a ranar Litinin, ya yin bikin ranar Ma’aikata, da aka gudanar, a buɗaɗɗen filin taro na Sani Abacha Stadium, da ke Ƙofar Mata, a jihar Kano.

Inda ya ce, ya na da yaƙinin cewar, Ubangiji ba zai kawo wani mutum da zai ruguza su ba.

Ganduje ya kuma yi waɗannan kalamai ne, a matsayin martani ga kalaman tsohon Gwamnan jihar, kuma Jagoran ɗarikar Kwankwasiyya, wacce ke gab da karɓar Mulkin jihar, ƙarƙashin jam’iyyar NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya ce, za su sake duba kan samar da Masarautun.

Gwamna Ganduje dai, ya karkasa Masarautun jihar zuwa guda biyar ne, tare da sauke Sarkin da ya riska a matsayin Sarkin Masarautar jihar, Malam Muhammadu Sanusi II, daga kujerarsa.

Da ya ke ƙarƙare jawabinsa na bikin ranar Ma’aikatan, Ganduje, ya ce sababbin Masarautun guda huɗu alama ce ta haɗin kai, cigaba, da ma inganta zamantakewar al’umma.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button