Ilimi
UTME: JAMB Ta Bada Damar Gyara Subject Combination
Hukumar shirya jarrabawar neman shiga manyan makarantu ta ƙasa (JAMB) ta buɗe shafin gyara subject combinations ga ɗaliban da su ka yi rijistar UTME ta kakar karatu ta 2024/2025.
Daga yanzu, dukkannin ɗaliban da su ka samu kura-kurai a fagen cike Combinations ɗinsu, su na da damar sauyawa zuwa dukkannin waɗanda su ke so.
Amma kafin hakan, akwai buƙatar ɗalibai su tabbatar da ingancin combinations ɗin da su ke son sauyawa, gudun maimaita kuskure.
Ku Sani: Subject Combination ɗin kowanne Course ya na iya sauyawa, daga wata makarantar zuwa wata.
Domin neman ƙarin bayani, ku tuntuɓi wannan lambar wayar : 08039411956
Rubutawar : Miftahu Ahmad Panda
08039411956.