UTME: YADDA ZA KU SAMU JAMB NOVEL NA WANNAN SHEKARAR
Rashin ba wa Ɗalibai JAMB NOVEL a CBT Centres, kamar yadda aka saba kowacce shekara, ya jawo ɗumbin tambayoyi kan matsayin amfani da Novel ɗin a wannan shekarar, tare da yadda za a same shi, da ma sunan Novel ɗin da za a yi amfani da shi.
***************************
Littafin THE LIFE CHANGER, na KHADIJAT ABUBAKAR JALLI, wanda aka yi amfani da shi a shekarun 2022 da 2023 dai, shi ne za a ƙara amfani da shi a wannan shekarar ma.
å YADDA ZA A SAME SHI
Abin mai sauƙi ne, hukumar JAMB ta samar da tsarin da kowanne Ɗalibi zai mallaki Littafin a matsayin Softcopy, ya yin da ɗaliban da ke da lalurar gani kuma, za su mallaki nasu Littattafan a tsarin sauraro na Audio Book.
• Da zarar Ɗalibi ya samo QR Code Scanner, ya yi scanning QR CODE / BAR CODE ɗin da ke jikin Registration Slip ɗinsa, kaitsaye zai tsinci kansa a shafin da zai sauke PDF na Littafin, akan Wayarsa ko Computer.
-Waɗanda basu da sukunin yin hakan kuma, kaitsaye za su iya tuntuɓarmu a wannan lambar wayar: 08039411956, domin mu tura musu PDF ɗinsa, mai kimanin shafuka 88 (39MB).
KU TUNTUƁI 08039411956, DOMIN TAMBAYA, KO NEMAN SHIGA ASOF JAMB GROUP.
Rubutawa: Miftahu Ahmad Panda.
08039411956