Waɗanda Su Ka Samu Aikin Yi Ne Kawai Za Su Biya Kuɗaɗen Bashin Ɗalibai – NELFund
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewar, dukkannin ɗaliban da su ka amfana da tsarin bashin ɗalibai na NELFund, za su fara biyan kuɗaɗen da su ka karɓa ne, shekaru biyu bayan kammala hidimar ƙasa (NYSC).
Babban Sakataren asusun na NELFund, Dr Akintunde Sawyer, shi ne ya bayyana hakan ya yin ganawarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), ranar Alhamis, a babban birnin tarayya Abuja.
Sawyer, ya ce dalilin sanya tsarin fara biya ɗin shekaru biyu bayan NYSC, shi ne domin bawa waɗanda su ka amfana ɗin wadataccen lokacin samun aikin yi, tare da shiryawa fara biya.
“Dokar ta yi tanadin cewar, dukkannin waɗanda su ka samu aikin yin da ake biyansu, za su fara biyan kuɗaɗen ne shekaru biyu bayan kammala NYSC, Amma hakan ba ya nufin ba za su iya biya kafin lokacin ba.
“Sannan, idan basu samu aiki shekaru biyu bayan kammala NYSC ɗin ba, shi ma ba zamu tilasta musu biya ba. A ina za su samo kuɗin?, zamu taimake su, tare da jiransu har zuwa lokacin da za su iya biya.
“Zamu samar da rijistar waɗanda su ka karɓi bashin, ta yanda masu bada ayyuka za su iya duba rijistar su ga su waye suke da bashin akansu.
“Da zarar sun ga wanda yake da bashi, kuma sun bashi aiki, zamu ɗora bayanansa a tsarin biyan bashin, ta yadda kaso 10 na abinda ya ke samu zai dinga komawa cikin asusunmu”, a cewarsa.
“Idan basu samu aiki ba, ko kuma sun rasa ayyukan nasu, ba wajibi ne su biya ba.
“Ba ƙoƙarin mayar da waɗanda su ka amfana da bashin zuwa ƴan ta’adda mu ke ba, muna ƙoƙarin tallafar ƴan Najeriya ne, domin samun ingantaccen Ilimi, ta yadda rayuwar al’ummar ƙasa za ta inganta, tare da haɓɓaka tattalin arziƙin al’ummarta”, a cewarsa.