Wani Ɗan Kasuwa A Uganda, Ya Auri Mata Bakwai, A Rana Ɗaya
Wani ɗan kasuwa a ƙasar Uganda, Habib Nsikonnene, ya auri mata bakwai, a ranar Lahadi, 10 ga watan Satumban da mu ke ciki.
Bayanin Auren nasa kuma, ya bayyana ne, bayan wallafa hotunan bikin da gidan Rediyon Capital FM su ka yi, a shafinsa na Twitter.
Sunayen Amaren da wannan Ango ya taki sa’ar Aura a rana guda su ne: Mariam, Madinah, Aisha, Zainabu, Fatima, Rashida, da Musanyusa, wacce ya bayyana a matsayin Uwargidansa, da su ka shafe tsawon shekaru bakwai su na gangarawa.
Biyu daga cikin Matan kuma, sun kasance ƴan uwansa na jini.
Rahotanni sun kuma bayyana yadda Nsikonnene ɗin ya gwangwaje Amaren nasa da sababbin Motoci ga kowaccen su.
Da ya jawabi a ya yin walimar Auren, ya yabawa Amaren nasa bisa kasancewarsu masu biyayya a gare shi, ya na mai cewa, “Matana su na da kyawawan ɗabi’u, kuma ko a junansu ma, ba sa baƙin kishi. Na gabatar da su a daban-daban, na kuma yanke shawarar Aurarsu baki ɗaya a lokaci guda, domin samar da faffaɗan Iyali. Har yanzu ni Matashi ne mai burin gina kyakykyawar gobe, da yardar Ubangiji, dan ba zance wannan shi ne ƙarshen matakin da zan taka ba”.