Zamantakewa

Wani Ɗan Kasuwa Ya Hallaka Kansa A Unguwar Sharada, Da Ke Kano

An yi tozali da gawar wani mutum mai shekaru 35 a duniya, Saleh Abdullahi, bayan da ya rataye kansa, a ɗakinsa, da ke unguwar Sharada, a birnin Kano.

Ɗan Kasuwar, ya kuma bar wani rubutu da ke ɗauke da jimlar “Ina baku haƙuri”. Sai kuma sauran rubutun da ke jikin takardar wanda ba ya karantuwa.

Matashin dai, na zaune ne a ɓangaren yara na gidan ɗan uwansa, mai suna, Idris Hamisu I.

Hamisun kuma, ya bayyanawa Manema Labarai cewar, “Na dawo daga Sallar Asuba, Matata ta tashi domin dafawa yaranmu abincin karyawa, tana ta neman ashana, amma bata samu ba. Sai ta tuna cewar, Saleh ya na amfani da ita, wajen kunna turaren wuta. Da ta tura yaronmu ya karɓo ashanar ne, sai yaran ya same shi a rataye, nan da nan kuma ya dawo wurinmu ya na ihun cewa, wani ya rataye Yaya Saleh. Cikin hanzari nima na tafi ɗakin, na kuma gani tabbas Saleh ɗin ne a rataye”.

Da aka tambaye shi, ko suna da wani saɓani da mamacin kafin wannan mummunan mataki da ya yanke hukuncin ɗaukarwa kansa, sai ya ce, “Bamu da wata matsala. Abin da kawai dai na sani shi ne, a ƴan kwanakin nan ya na cikin damuwa, kuma a matsayinmu na ƴan kasuwa, dukka nasan muna tsintar kanmu a irin wannan yanayin, idan kasuwa babu kyau.

“Mu ƴan kasuwa ne, muna harkar kayayyakin katako ne, amma a wasu lokutan shi Saleh ya na shiga harkar saye da sayarwar tsofaffin kayayaki.

“Ya nuna alamun damuwa a kwanakin nan, saboda ya karɓi kuɗin wani mutum, ya kuma sayo kaya har na Naira 400,000 daga wasu mutane a Rijiyar Zaki, inda su ka kaishi wani gida da su ka ajiye kayan, su ka kuma sanar da shi cewar, ya koma washe gari ya ɗauka. Da ya tambayi lambar wayarsu, sai su ka ce masa, tun da ya riga ya ga gidan, kawai zai iya komawa a koyaushe, sai dai da ya koma daga baya, sai ya rasa gidanma baki ɗaya. Hakan ne ya jefa shi cikin damuwa, saboda kuɗaɗen ba nasa bane, kuma masu shi sun dame shi akan ya biya”.

Har ya zuwa lokaci haɗa wannan rahoto kuma, rundunar ƴan sandan jihar ta Kano, ba ta ce komai kan lamarin ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button