Ƙasashen Ƙetare

Wani Fasto Ya Umarci Mabiyansa Su Yi Ta Azumi, Har Sai Sun Mutu

An tsinci gawarwakin mutane 21 a wani fili, mallakin wani shugaban coci, a ƙasar Kenya, bayan da faston ya umarci magoya bayansa, da su yi ta yin Azumi, har sai sun mutu, domin ganin Jesus.

Jami’an ƴan sanda sun kuma bayyana cewar, har ya zuwa yanzu basu ba a kai ga samun damar haƙa wasu kaburburan a filin Mallakin Fasto Paul Makenzi, wanda aka yi ram da shi tun a ranar 14 ga watan Afrilu ba, bisa tuhumarsa da wasu laifuffuka da ke da alaƙa da tsafe-tsafe.

Makenzi ya kuma shafe sama da kwanaki huɗu cikin halin yunwa, ya yin da ya ke cigaba da kasancewa a tsare, a hannun Jami’an ƴan sanda. Kafin yanzu an kuma cafke shi har karo biyu, tun a shekarar 2019, da kuma a watan Maris ɗin wannan shekarar, dukka bisa tuhume-tuhumen da ke da alaƙa da mutuwar ƙananan yara. Kuma a dukkannin shari’un biyu an damƙa shi ne a hannun beli, ya yin da kotu ke cigaba da sauraron ƙararrakin.

Ƴan siyasar cikin gida kuwa, na cigaba da kiraye-kirayen ganin ba a sake shi ba, a wannan lokacin, su na masu kokawa da yawaitar haɓɓakar ayyukan tsafi, a yankin Milindi.

Tsafe-tsafe dai, abu ne da ya zama ruwan dare, a ƙasar ta Kenya, inda a mafi yawan lokuta ake aiwatar da shi, da sunan Addini.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button