Tsaigumi

Wani Magidanci Ya Zargi Shugaban Cocin Da Ya Ke Ibada, Da Ɗirkawa Matarsa Ciki

Ana zargin shugaban Cocin Christ High Commission Church, Araromi-Ugbesi, da ke Umuo-Oke, na jihar Ekiti, Pastor Noah Abraham, da sace wata Matar Aure, tare da yi mata ciki.

Wani mai Ibada a cocin, mai suna, Dare Ikuenayo ne, ya bayyana wannan zargi, ya yin da ya ke zantawa da Jaridar Vanguard, ya na mai ƙarawa da cewar, Abraham ɗin ya sanar da cewa shi ne ya ɗauke matarsa, kuma babu abin da wani mutum ya isa ya yi.

Ikuenayo ya ce, Limamin Cocin ya sace masa Matarsa, kuma uwar ƴaƴansa guda uku ne, bayan da ya sanar da shi cewar, ta samu tagoshin rabauta da falala, dan haka ya barta ta zauna da shi.

“Na shiga wata Coci da ke Kabba, a jihar Kogi, amma wata rana kwatsam, sai Limamin Cocin ya kira ni, tare da sanar da ni cewar, Matata ta rabauta da falala daga Ubangiji, dan haka ana buƙatar na barta ta zauna da shi tsawon wata guda, domin ta samu damar bauta da biyayya ga Ubangiji”, a cewar Ikuenayo.

“Kwatsam sai na fara ganin Matata ko kulani ma ta daina son yi, ballantana ganina. Da na yi yunƙurin yin magana kan lamarin, sai Limamin ya bayyana a cikin Coci cewar, ya ɗauke Matata, kuma babu wanda ya isa ya ƙwatota daga wurinsa. Na yi iya bakin ƙoƙarina, amma yaƙi, har sai da ya yi mata ciki, ya kuma mayar da ita cikin gidansa sosai”.

Tuni dai, rundunar ƴan sandan jihar ta Ekiti, haɗin guiwa da hukumar yaƙi da safarar bil-Adama ta ƙasa (NPTIP), su ka cika hannunsu da Abraham ɗin, bisa zarginsa da sace sama da mutane tara, cikinsu kuma har da ƙananan yara.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button