Zamantakewa

Wani Makiyayi Ya Sare Hannun Manomi A Bauchi

Ana zargin wani Makiyayi mai shekaru 15 a duniya, Adamu Ibrahim, da sare hannun wani Manomi na hagu, a ya yin wata sa’in’sa da aka fuskanta a tsakaninsu, ranar Asabar, a jihar Bauchi.

Lamarin dai, ya faru ne a ƙauyen Jital, da ke kan titin Gombe. Inda tun da farko aka zargi Makiyayin da kora shanunsa cikin gonar manomin, ta Shinkafa.

Inda Jami’an ƴan sanda su ka ce, bayan zuwan Manomin gonarsa ne kuma, sai rikici ya ɓarke, Wanda har ya kai ga sare hannun Manomin, daga wancan matashin Makiyayi.

Tuni Jami’an ƴan sanda kuma, su ka yi ram da Makiyayin jim kaɗan bayan aukuwar wannan lamari.

Inda kuma aka garzaya da Manomin da aka sarewa hannun, zuwa Asibitin koyarwa na Tafawa Balewa (ATBUTH) da ke Bauchi, inda ya ke cigaba da samun kulawar Likitoci, har ya zuwa wannan lokaci.

Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar ta Bauchi, ya bayyanawa Manema Labarai a ranar Asabar cewar, tuni rundunarsu ta ƙaddamar da bincike kan aukuwar lamarin.

Ya kuma ce, an ɓoye sunan Manomin da aka sare wa hannun ne, saboda dalilai na tsaro.

Ko a ranar Asabar ɗin da ta gabata dai, sai da Kwamishinan rundunar ƴan sandan Jihar, Auwal Mohammed, ya gargaɗi makiyayan da su dinga ƙauracewa faɗawa gonakin manoma, ya na mai tabbatar da cewar za su tabbatar da dukkannin wanda aka samu da aikata irin hakan, ya fuskanci hukunci.

Su kuwa Manoman Jihar, buƙatarsu ya yi da su dinga ƙauracewa ɗaukar doka a hannayensu; a madadin hakan, ya shawarce su da su dinga kai rahoton dukkannin wani laifi da aka aikata musu zuwa Ofishin rundunar ƴan sanda mafi kusa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button