Wani Mutum Ya Faskara wa Kakarsa Gatari, Bayan Da Ta Ƙi Mutuwa Tsawon Shekaru 100
Wani mutum mai shekaru 37 a duniya, da ke zaune a birnin Estonia, na ƙasar Jamus, ya kashe kakarsa ta hanyar faskara mata Gatari, sakamakon ƙosawar da ya yi da taurin ranta, bayan da ta shafe tsawon shekaru 100 a duniya.
Mutumin dai, ya hallaka kakar tasa da ke lallaɓa rayuwa akan keken guragu (Wheelchair) ne, a gidanta da ke Hamburg, da safiyar ranar 6 ga watan Maris, inda kuma ya miƙa kansa ga Jami’an ƴan sanda, ba tare da wahalar da Shari’a ba.
Kuma tuni, aka gurfanar da shi a gaban wata Kotu, da ke Arewacin birnin Hamburg, na ƙasar ta Jamus, bisa tuhumar kisan kai.
Inda Lauyan tsohuwar ya ce, jikan ya miƙa kansa ga hukuma ne, bayan da ya gaza samun nutsuwa sakamakon hallakata.
Tsohuwar mai fama da ciwon taɓin hankali, ta sha sara a wurare sama da 16 a kai da wuyanta, a yunƙurin da ta yi na kare kanta.
A cewar masu gabatar da ƙara, bayan aukuwar hakan ne kuma, sai Dattijuwar ta faɗo ƙasa, inda shi kuma ya yi amfani da damar wajen karya kafaɗarta.
Ta kuma rasa ranta, sakamakon matsalar tsinkewar laka.
A nan ne kuma, Mutumin ya kira layin taimakon gaggawa, tare da bayyana musu wannan ɗanyen da ya aikata na hallaka kakarsa, wacce ta ƙarasa shurawa bayan isar Jami’an ƴan sanda.
Inda mutumin ya miƙa kansa ga hukuma, ba tare da neman matsera ba.