Kotu

Wani Mutum Ya Maka Asibiti, Da Gwamnatin Delta A Gaban Kotu, Sakamakon Rasa Ran Matarsa

An maka Babban Asibitin Eku, da ke jihar Delta, Shugabar Asibitin, Tawagar Likitoci, da ma Gwamnatin jihar a gaban Babbar Kotun jihar Delta, bisa zarginsu da yin sake da aiki, wanda ya sanya wata mata mai suna, Mrs. Anesther Egede, mai shekaru 33 a duniya ta rasa ranta.

Ta cikin sammacin da Kotun ta aike musu, a ranar Lahadi, mai ɗauke da lambar ƙara, HCI/44/2023, Kotun tace ƙarar na tsakanin Mr. Festus Godson Egede a matsayin mai ƙara ne, ya yin da waɗanda ake ƙara su ka haɗar da, Babban Asibitin Eku, Gwamnatin Jihar Delta, Shugabar Asibitin, Dr Totibo, da ma sauran waɗanda aka bayyana a cikin ƙunshin ƙarar.

Mijin mamaciyar, Godson Egede, ya zargi Dr. Totibo ne dai, da barin curin auduga a marar Matarsa, bayan kammala yi mata aikin tiyata, wanda hakan ya yi sanadiyyar rasa ranta baki ɗaya.

Ya na mai cewar, “Matata, Mrs. Egede Anesther, ta ji ciwo ne a mararta, sai ta garzaya zuwa Asibitin Obiaruku, inda anan ne aka yi mata hoton marar, kamar yadda Likita ya buƙata.

“Bayan an yi kuma, sai Asibitin su ka gano cewar, ta na da Appendicitis ne.

“Kuma su ka ce, Appendicitis ɗin bai haura kaso 7.6 ba, dan haka bai iso matakin da za a iya yi mata ƙara min aiki ba.

“Aka kuma sallameta daga Asibitin na Catholic, bayan kwana biyu da kwantar da ita, Likitan da ya lura da lafiyarta, ya ce mu cigaba da kula, domin ciwon bai isa aiki ba.

“Bayan mun koma gida, sai ciwon ya ƙara yin tsanani, hakan ya sa na kaita Babban Asibitin Eku, domin sake duba ta sosai, tunda tuntuni an gano cewar, Appendicitis ne.

“A babban Asibitin, mun samu wani Likita mai suna, Dr. Ebom Totibo, wanda ya umarce mu da mu sake yin wani Scanning ɗin.

“Dr. Totibo ɗinma ya shawarcemu da mu je P. Wave Scan, domin yin hoton, kuma bayan an yi, shi ma Likitan ya yi ƴan gwaje-gwajensa akan matata, sai ya ce mu koma washe gari, domin a yi mata aikin cire appendicitis ɗin.

“Washe gari mu ka koma, aka kuma yi mata aikin.

“Bayan an kammala, sai shugaban tawagar Likitocin, Dr. Ebom Totibo, ya ce min matartawa ta na da matuƙar kitse da ƙiba, a sakamakon hakan, hanjinta ya rufe appendicitis ɗin, dan haka ba a cire shi ba.

“Inda ya cigaba da cewa, a madadin hakan, Likitocin sun sake wa hanjin nata shiri”.

Egede, ya kuma ƙara da cewar, bayan yin aikin ne, sai aka tura matar tasa zuwa sashen jinya, haka kuma aka yi ta samun cigaba a lafiyartata, har mararta ta warke, amma tsawon kwanaki 14 ba ta iya tsaiwa.

“Sai guda daga cikin Likitocin da su ke aiki a Asibitin ya buƙaci a yi hoton MRI, domin gano matsayin aikin da aka yi mata.

“Hakan kuwa aka yi, an yi mata MRI Scan, a Asibitin Lily, da ke Benin City, na jihar Edo, inda sakamakon ya gano cewar, Dr. Ebom da tawagarsa, sun manta curin auduga a marar Matata, bayan yi mata aiki, wanda shi ne ma ya yi sanadiyyar rasa ranta”, a cewarsa.

Ya kuma ce, tuni a matsayinsu na Iyalanta su ka maka Asibitin ƙara, bisa zargin wasa da aiki.

Ya yin da aka tuntuɓi, Shugabar Asibitin na Eku, Dr Mrs Etaghene Harietta, sai ta ce ba zata iya cewa komai a yanzu ba, amma manema labarai za su iya tuntuɓar ma’aikatar lafiya.

“Ba zan iya magana kan wannan batun ba, ku miƙa tambayoyinku zuwa ga babban reshenmu da ke Asaba”.

Kuma, dukkannin yunƙurin manema labarai, na tattaunawa da Kwamishinan lafiyar jihar, Dr. Joseph Onojaeme abin ya ci tura, bayan da aka gaza samunsa a waya, kuma har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, bai bada amsar gajeren saƙon da aka aike masa ba.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button