Zamantakewa

Wani Mutum Ya Mutu A Rijiya, Ya Yin Da Ya Ke Yunƙurin Taimako, A Kano

Wani mutum mai shekaru 37 a duniya, Umar Ayuba, ya rasa ransa a cikin wata rijiya, da ke unguwar Kawon Maigari, a ƙaramar hukumar Nasarawa, ta jihar Kano.

Kakakin hukumar kashe gobara na jihar, Umar Ayuba, shi ne ya tabbatar da aukuwar lamarin, ga kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), a jihar Kano.

Inda Abdullahi ɗin ya ce, wannan lamari ya auku ne, da yammacin ranar Talata.

“Mun samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 5:20 na yammaci, daga wani mutum mai suna, Mamuda Abdallah, wanda ya bayyana mana cewar, wani Bawan Allah ya faɗa rijiya.

“Nan da nan kuma mu ka aike da tawagar Jami’anmu, inda su ka isa wurin da misalin ƙarfe 5:32 na yammaci,” a cewarsa.

Kakakin ya kuma ƙara da cewar, Wata mata ce ta buƙaci mamacin da ya taimaka ya fito mata da rafofinta da su ka faɗa rijiyar.

A cewarsa kuma, nan da nan ne Jami’an nasu su ka garzaya da shi zuwa Asibiti saboda rashin wadatacciyar iskar Oxygen da ya ke shaƙa.

Ya na mai cewar, “An garzaya da mutumin zuwa Asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad, inda a nan ne Likita ya tabbatar mana da cewar, ya rasa ransa.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button