Wani Mutum Ya Sarewa Maƙwacinsa Tsintsiyar Hannu, Bisa Zargin Kwanciya Da Matarsa
Wani Manomi, mai suna, Oro Umaru, da ke sansanin Fulani na Ba’abete, a ƙaramar hukumar Kaiama, ta jihar Kwara, ya gurfana a gaban Babbar Kotun Majistirin jihar Kwara, da ke da matsuguni a Ilorin, a ranar Alhamis, bisa zarginsa da yunƙurin kisan kai.
Ana zargin Umaru ne dai, da sare hannun wani maƙwabcinsa, wanda su ke zaune a Rigar Fulani ɗaya, mai suna, Abubakar Sanda, bisa zarginsa da aikata baɗala da Matarsa.
Ana kuma tuhumarsa ne da laifi guda ɗaya a gaban Kotun, na yunƙurin kisan kai, wanda ya saɓa da sashe na 299 na kundin Penal Code.
Ƙunshin bayanan rundunar ƴan sanda, ya bayyana cewar, ɗan uwan wanda lamarin ya rutsa da shi, mai suna, Sanda Mohammed ne, ya shigar da rahoton aukuwar lamarin, a rundunar ƴan sanda.
“A ranar 08 ga watan Satumban 2023, da misalin ƙarfe 20 da mintuna 30, wani mutum mai suna, Sanda Mohammed, na Rigar Ba’abete, da ke ƙaramar hukumar Kaiama, ya shigar da ƙorafi a ofishin rundunar ƴan sanda cewar, a wannan ranar da misalin ƙarfe 12:00, ya yin da ƙaninsa mai suna, Abubakar Sanda, wanda su ke zaune a gida guda, ya ke dawowa gida daga kasuwar Kara ta Kaiama, sai wani mutum, wanda shi ma a rugarsu ya ke zaune, mai suna, Oro Umaru ya tsare shi, tare da sare masa hannunsa na dama.
“Hakan ne kuma ya sanya rundunar ƴan sanda ta yi gaggawar kama ka, Oro Umaru. A ya yin da ake bincikarka a ashen binciken manyan laifuka (CID) kuma, ka bayyana cewar, kuna rayuwa ne a wuri guda, Amma wani lokaci a shekarar 2022, ka zargi Abubakar Sanda ɗin da aikata rashin gaskiya da Matarka, Fatima Oro, ka kuma kama su a lokuta da dama, inda har ka shigar da ƙorafin hakan ga Mahaifinka, mai suna, Alhaji Hamadu, amma ba a yi komai ba.
“Ka kuma ƙara bayyana mana cewar, ko a ranar 06 ga watan 09 da misalin ƙarfe 22 ma, sai da ka kama Abubakar Sanda ɗin ya na hira da Matarka, Fatima, inda ganin kana nufowa wajen da su ke ne ma, ya sanya Abubakar Sanda ɗin ya ari ta kare.
“Ka kuma bayyana mana cewar, a ranar 08 ga watan Satumban da mu ke ciki, ka farmaki, Abubakar Sanda ɗin, a gidansa, inda har ta kai ga ka sare masa tsintsiyar hannun dama, tare da ji masa rauni a goshinsa”, a cewar takardar ƙarar.
Kuma kotun ba ta samu jin ta bakin Wanda ake zargin ba, Amma Ɗan Sanda mai gabatar da ƙara, Gbenga Ayeni, ya roƙi kotun da ta aike da wanda ake zargin zuwa gidan gyaran hali, haf zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Da ya ke bayyana matsayar Kotun, Mai Shari’a Gbadeyan Kamson, ya umarci da a tsare wanda ake zargin, tare da ɗage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar, 11 ga watan Oktoban 2023.