Zamantakewa

Wani Mutum Ya Shaƙe Budurwarsa Mai Ciki, Har Ta Mutu, A Kano

Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta samu nasarar daƙume wani mutum mai suna, Phibus Ibrahim, bisa zarginsa da hallaka budurwarsa mai shekaru 22 a duniya, Theresa Yakubu.

Ibrahim, wanda ya aikata wannan ɗanyen Aiki, a ƙaramar hukumar Tudun Wada, ta jihar Kano, ya shiga hannun hukuma ne, tare da abokin cin mushensa, Gabriel Bila, dukkanninsu mazauna, Unguwar Korau, da ke ƙaramar hukumar Tudun Wada.

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Mamman Dauda, ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN), aukuwar lamarin, a ranar Talata.

Inda ya ce, wannan aika-aika ta faru ne, a ranar 2 ga watan Afrilu, da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, inda rundunar tasu ta samu rahoton tsintar gawar mamaciyar, yashe a gefen titin Kano zuwa Jos, da ke ƙauyen Anadariya.

”Bayan samun wannan rahoto ne kuma, sai aka tashi tawagar Jami’an ƴan sanda, zuwa wurin da lamarin ya auku, inda su ka ɗauki mamaciyar zuwa Babban Asibitin Tiga, wanda anan ne Likita ya tabbatar da rasuwarta.

”Kuma bayan ƙaddamar da bincike ne, sai aka gano cewar, matashiyar ta bar Nassarawan Kuki ne, zuwa ƙauyen Yantomo, da ke ƙaramar hukumar Garin Malam, a jihar Kano, a ranar 27 ga watan Mari’s, da misalin ƙarfe 6:00 na yammaci.

”Kuma bayan ƙara zurfafa bincike, an samu nasarar daƙume babban wanda ake zargi, wanda kuma ya amsa aikata laifinsa, ya na mai cewar, ya yi amfani da veil ɗin mamaciyar ne, wajen shaƙeta.

Dauda, ya kuma ce, za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya, da zarar sun kammala gudanar da bincike.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button