Wani Saurayi Da Ya Hallaka Budurwarsa Cikin Sirri, Ya Sanya Hoton Gawarta A Status
Wasu rahotanni da ke fitowa a yau (Asabar), daga rundunar ƴan sandan ƙasar India, sun bayyana yadda wani matashin ɗalibi, mai shekaru 20 a duniya, da ke karatun aikin jiyya (Nursing), ya hallaka budurwarsa, a Hotel ɗin Chennai, da ke ƙasar ta India, ya kuma ɗauki hoton gawar, tare da sanyawa a WhatsApp status.
Chennai dai, wani babban birni ne, da ke yankin Kudancin India.
Jaridar India Today, ta rawaito cewar, an gano makashin ne, bayan da ƙawayen budurwar da aka hallaka, su ka tsinkayi hoton gawar matashiyar mai suna, Ashiq, a status ɗin makashin.
Jami’an ƴan sanda, sun tsinci gawar matashiyar a ɗakin hotel ɗin da ya hallakata, bayan da ƙawayen nata su ka kwarmata batun.
A cewar hukumomin da abin ya shafa dai, wacce aka kashe ɗin ɗalibar aji biyu ce a sashen karatun Aikin Jiyya (Nursing), kuma sun shafe tsawon shekaru biyar suna tsinkar furen soyayya da makashin nata.
Shaƙuwarsu ma har ta kai matakin da su ka kama ɗaki tare, su ke zaune a birnin na Chennai.
Fusataccen matashin kuma, ya hallaka budurwar ne, bayan da su ka yi musayar yawu, kan zarginsa da ta yi da yin wata budurwar bayan ita, saboda fashin zuwa ajin da ya yi na tsawon kwanaki uku, inda ya kama musu ɗakin Hotel da nufin zuwa ko za a samu sasanci.
Amma kwatsam sai ƙawayenta su ka tsinci hoton gawar matashiyar a status ɗinsa.
Bayan ƙaddamar da binciken da Jami’an ƴan sanda su ka yi ne kuma, sai su ka gano gawar matashiyar a Hotel ɗin mai zaman kansa. Inda bidiyon da na’urar CCTV ke ɗauka kuma, ya nuna musu zahirin yadda aka hallakata.
Tuni kuma matashin ya amsa laifinsa bayan ya shiga hannu.
Rahotanni dai, sun bayyana cewar, matashin ya yi amfani da rigarsa ne, wajen shaƙe wuyanta, har tace ga garinku nan.