Warwarar Rahoto: Kaso 6 Cikin 10 Na Dukkan Ɗaliban Kano, Su Na Shan Miyagun Ƙwayoyi – NDLEA
Hukumar hana Sha da fataucin Miyagun Ƙwayoyi NDLEA, ta yi warwara kan wani rahoto da ta fitar, wanda ke bayyana cewar, Ɗalibai 6 ne ke shaye-shaye cikin dukkannin Ɗalibai 10, da ke jihar.
Kwamanda Sifiritanda na rundunar, Jibril Ibrahim, ya kuma bayyana cewar, adadin matasan da ke shaye-shaye daga cikin ɗaliban ya yi matuƙar yawan gaske, inda ya ce akwai yiwuwar adadin ya kai kaso 50 cikin 100 a nan gaba kaɗan.
Sai dai, da ya ke fashin baƙi kan rahoton, Kakakin rundunar ta NDLEA, Sadiq Muhammad Maigatari, ya ce sun fitar da alƙaluman ne, dogaro da yawan matasan da su ke da su a Cibiyar Gyaran tarbiyya ta hukumar.
Ya na mai cewar, “Bayanai sun zo gare mu kan cewar, ƙididdigar da guda daga cikin Jami’anmu ya fitar, game da yawaitar shaye-shayen Miyagun Ƙwayoyi a tsakanin ɗalibai ba dai-dai bane, kuma muna masu sanar da Jama’a cewar, za mu fitar da sahihan alƙaluma kan lamarin, a nan kusa.
“Ƙididdigar da aka fitar, wacce ke cewa, cikin dukkannin Ɗalibai 10, biyar zuwa shida su na amfani da Miyagun Ƙwayoyi, an fitar da ita ne, bisa la’akari da matasan da ke Cibiyar Gyaran tarbiyyarmu. Saboda haka muna masu bada haƙuri kan matsalolin da ƙididdigar ka iya haifarwa.”