Wasanni: Yadda Kano Pillars Ta Sha Kashi A Hannun Akwa United
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, ta samu rashin nasara a wasan da suka fafata tsakaninta ƙungiyar Akwa United a wasan mako na 32 na gasar Firimiya ta ƙasa, wanda ya gudana a filin wasan ƙasa da ƙasa na Godswill Akpabio.
Ƙungiyar kano pillars mai laƙabin ‘Sai Masu Gida’ dai, ta yi rashin nasara ne da ƙwallaye uku da nema (3-0).
Ɗan wasan Akwa United, John Ubong Friday, shi ne ya fara jefawa ƙungiyarsa ƙwallon farko a mintuna na 35, bayan samun bugun daga kai sai mai tsaron raga.
Jim kaɗan bayan dawo wa daga hutun rabin lokaci, a mintuna na 59 Ɗan wasan Akwa, Jonh Ubong friday ya sake jefa ƙwallonsa ta biyu, a ragar Kano Pillars.
Bayan ƙarewar mintuna 90 da aka warewa wasan ne kuma, sai aka ƙara mintuna 5, wanda cikin minti na 94 Akwa United ɗin ta ƙara ƙwallo ta 3, ta hannun Ɗan wasanta, Said Mubarak.
Haka kuma aka tashi daga wasan, Akwa United na da ƙwallo uku, yayin da Kano Pillars ta ke nema.
Zuwa yanzu dai, Pillars tana mataki na 9 ne, a teburin gasar, da maki 44, ya yin da Akwa United ke a matsayi na 16 da maki 37.
A gefe guda kuma, za a tafi hutun wata ɗaya a gasar, domin bawa Rivers United damar kammala kwantan wasanninta guda biyar, da take bi bashi,
A wasa na gaba, Kano Pillars za ta karɓi baƙuncin Doma United ne, a wasan mako na 33 da zai gudana a buɗaɗɗen filin wasa na, Sani Abacha, da ke Ƙofar Mata.
Sai har yanzu ana dakon rana da lokacin wasan, wanda za a sanar, da zarar hukumar shirya gasar ta fitar da sabon jadawalin ragowar wasanni 6 da su ka rage, kafin kammala gasar baki ɗaya.
Ana sa ran cigaba da gasar, a tsakanin ranakun 25 zuwa 26 na watan Mayun 2024, mai kamawa.