Wasannin Afirka: Najeriya Ta Koma Matsayi Na 3, Bayan Fafata Wasan Rana Ta 7
Bayan samun nasarar lashe tagulla a rana ta 7, na wasannin ƙasashen Afirka, da ke cigaba da gudana a Ghana, Najeriya ta koma matsayi na uku, akan teburi, bayan da Afirka ta Kudu ta ɗare matsayi na biyu, da Najeriyar ke kai a baya.
Najeriya ta fara fafata wasannin rana ta 7 ne, a matsayin ta 2, bayan da ta mallaki jerin kyaututtuka 54 (Zinare 22, Silver 13, da Tagulla 19), inda ta ƙare wasannin a matsayi na uku.
Rashin takar sa’a a wasannin nata na ranar Alhamis kuma, ya sanya Afirka ta Kudu ɗarewa matsayi na biyu, bayan lashe kyaututtukan zinare uku, silver biyu, da kuma tagulla ɗaya, dukka a rana guda.
A yanzu kuma, dukkannin ƙasashen sun mallaki kyaututtukan zinare kai ɗaya ne, ya yin da Afirka ta Kudun ta zarce Najeriya da Kyaututtukan Silver 22, ya yin da Najeriyar ke da 13.
Dukkanninsu kuwa, su na da doguwar tazara tsakaninsu da ƙasar Egypt, wacce ta lashe kyaututtuka 115, da su ka haɗarda Zinare 65, Silver 27, da tagulla 23.