Zamantakewa

Wasu Iyalai Sun Yi Watsi Da Akwatin Gawar Da Surukinsu Ya Saya Domin Binne Surukarsa, Bayan Da Su Ka Ce ‘Akwatin Mummunace’

Wasu Iyalai, da ke zaune a Tombo Mbatie, da ke ƙaramar hukumar Buruku, ta jihar Benue, sun yi watsi da akwatin gawar da surukinsu ya saya, domin binne gawar Surukarsa (Mahaifiyar Matarsa).

Wani mai amfani da kafar sadarwa ta Facebook, mai suna, Bem Raphael Aondongu ne dai, ya bayyana hakan, ta shafinsa, a ranar Alhamis.

Inda ya ce, Iyalan sun ƙi karɓar Akwatin gawar ne saboda rashin kyawunta, da kuma ganin cewar sun fi ƙarfin a binne gawar danginsu a cikinta.

Inda Aondongu ɗin yace ”Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar yau, inda wasu Iyalai da bazan bayyana ko su wanene ba, su ka gaza karɓar Akwatin gawar da Surukinsu ya saya, domin binne surukarsa.

”Kamar yadda al’adar TIV ta ke dai, idan Uba ko Uwa su ka mutu, to ƴarsu mace ta farko, da ta yi Aure ce ke da alhakin samar da Akwatin da za a binne gawar Iyayen.

”Kuma domin cigaba da kimanta wannan al’ada ne, sai Macen ta farko ta buƙaci Mijinta da ya samar da Akwatin da za a sanya Mahaifiyarta ta, amma bayan ya yi ƙoƙarin samar da akwatin da hotonta ke ƙasa, sai su ka ƙi karɓa.

”Inda Iyalan Mamaciyar su ka ce, akwatin bata da kyau, dan haka ba za a binne wacce ta fito daga danginsu a cikinta ba”.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button