Wata Ƙungiya Ta Ƙaddamar Da AI Na Fannin Shari’a
A ƙoƙarinta na tabbatar da sauƙaƙuwar al’amuran shari’a ga jama’ar Najeriya, ta hanyar amfani da fasahohin zamani, wata ƙungiya mai zaman kanta, mai suna, Citizens Gavel, ta ƙaddamar da ƙirƙirarriyar fikira (Artificial Intelligence) irinta ta farko, a fannin shari’ar Najeriya.
Ƙaddamar da AI ɗin, wanda ya gudana a babban birnin tarayya Abuja, an yi masa take da “AI For Justice: Highlighting The Innovative Use Of AI In The Legal Sector And It’s Potential To Revolutionise Access To Justice.”
Da ya ke jawabi a ya yin taron, Fitaccen Lauyan nan mazaunin Lagos, kuma jagoran gudanar da ayyukan ƙungiyar ta Citizen Gavel, Oluwafemi Ajibade, ya ce an samar da AI ɗin ne, domin taimaka al’umma wajen samun kusanci da al’amuran shari’a, tare da magance musu matsalolinsu, da ke alaƙa da fannin na shari’a.
Ajibade, ya kuma ce, AI ɗin wanda aka sanya suna ‘PODUS’, an horas da shi ne kan abubuwan da ke da alaƙa da matsalolin ko ta kwana, lamuran da su ka shafi ƴan sanda, cin zarafi ko azabtarwa, lamuran da su ka shafi haƙƙoƙin al’umma, kama mutane ba bisa ƙa’ida ba, tare da tsare su ba akan doron doka ba.
Ya kuma ƙara da cewar, ba an samar da AI ɗin ne, domin ƙwace aikin shari’a daga hannun Lauyoyi ba, sai dai domin ya tallafa, tare da sauƙaƙa musu wajen gudanar da ayyukansu.
Domin sauƙaƙa amfani da AI ɗin kuma, ƙungiyar ta sanya damar saduwa da shi ta hanyar WhatsApp, sai dai hakan bai hana samun damar mu’amala da shi ta shafin Website ba.