Kotu

Wata Mata Ta Buƙaci Kotu Ta Datse Igiyar Aurenta, Saboda Rikicin Cikin Gida

Wata mata ƴar kasuwa, mai suna, Anthonia Ubong, ta roƙi Kotun sauraron shari’un Zamantakewa, da ke zaune a Jikwoyi, na babban birnin tarayya Abuja, da ta roƙar mata Mijinta ya sake ta, sakamakon rikicin cikin gida, da ya tsananta a tsakaninsu.

Anthonia, ta yi wannan roƙo ne, a ranar Litinin, ya yin da ta ke bayyana dalilanta, kan rashin amincewar sawwaƙe mata, da Mijinta mai suna, Mr Ime, ya gabatar ga Kotun.

Anthonia dai ta ce, “Mijina ba ya bani abinci. Dukan idon sawuna ma ya yi, lokacin da na buƙaci ya bani Naira 100 domin na sayi abinci, ya yin da nake da tsohon ciki har na tsawon watanni takwas. Ban daina jin zafin idon sawun nan nawa ba, har lokacin da na haihu.

“Sannan ya ƙi biyan Naira 60,000 da aka buƙata domin a yi min aikin fito da abin da na haifa, domin na sha fama da doguwar naƙuda. Mahaifiyata da Ƴar Uwata ne su ka biya kuɗaɗen Aikin nawa, kuma su ka cigaba da kula da ni. Mijina Naira 4,000 kawai ya bani.

Ta kuma ƙara da bayyana yadda Mijin nata ya nausheta a fuska, wanda har sai da ya gotar mata da ƙashin muƙa-muƙi, ta kuma ce, ya girmeta da shakaru 11, amma sam ba ya barinta tace ko da uffan game da zaman Auren nasu.

Matar, ta roƙi kotun da ta rushe Auren nasu, tare da bata damar kula da Jaririnsu guda ɗaya da su ka haifa.

Alƙaliyar Kotun, Mai Shari’a Thelma Baba, ta ɗage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 28 ga watan Satumban da mu ke ciki, domin jin ta bakin dukkannin ɓangarorin.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button