Zamantakewa

Wata Mata Ta Buƙaci Kotu Ta Raba Aurenta Da Mijinta, Saboda Rashin Sha’awa

Wata mata mai suna, Hassana Adamu, ta buƙaci babbar kotun Gwagwalada, da ke Abuja, da ta raba Aurenta da ya shafe shekaru 10, da Mijinta, Danjuma Ali, bisa rashin son Mijin, tare da daina sha’awar Aurensa.

Hassana, wacce ke zaune a yankin Kwali, na babban birnin tarayya Abuja, ta kuma bayyanawa kotun cewar, sun samu ƙaruwar yara uku, tsakaninta da Mijin nata.

”Na gaji da Auren nan, kuma bana ƙaunar Mijina ko kaɗan, a yanzu.

”Mijina ya yi watsi da ni, ba kuma ya shiga ɗakina, hasalima ko sha’awata ba ya yi. Ina son kotu ta raba wannan Aure saboda rashin soyayya da sha’awa”.

Sai dai, a nasa martanin, Ali ya ce har yanzu ya na ƙaunar matarsa.

Inda kuma, Alƙalin kotun, Abdullahi Abdulkarim, ya shawarci Ma’auratan da su je su sasanta junansu.

Kuma Alƙalin ya tambayi mai ƙarar cewar, ko za ta iya cigaba da zama da Mijin nata idan ya gyara dukka kura-kuransa ?, Inda ta kaɗa baki ta ce ”A’a”.

Kuma tuni kotun ta ɗage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Mayu.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button