Wata Mata Ta Buƙaci Mijinta Ya Sauwaƙe Mata, Saboda Yawan Wasa Da Al’aurarsa
Wata Mata, da ke gudanar da kasuwancinta, a babban birnin tarayya Abuja, Doris Unekwu, ta roƙi Kotun sauraron shari’un Iyalai, da ke Jikwoyi, a babban birnin tarayya Abuja, da ta raba Aurenta da Mijinta, saboda gaza sauke haƙƙinta da ya ke.
Ta cikin takardar buƙatar sauwaƙe matan da ta gabatarwa Kotun, Matar ta ce Mijinta mai suna, Matthias, ya na biyawa kansa buƙata ta hanyar wasa da gabansa, wanda hakan ke da matuƙar illa ga lafiyar ƙwaƙwalwa da gangar jikinsa, ba ya ga tauye mata haƙƙoƙinta, da ya ke yi.
“Mijina ya daina tarawa da ni, na yi iya bakin ƙoƙarina, amma ya ƙi.
“Na taɓa kamashi ya na wasa da gabansa. Da na tambaye shi me yasa, sai ya ce min, ya ga wani abu ne a yanar gizo, ya ke son ya gwada”, a cewarta.
Matar ta kuma ce, Mijin nata baya dawowa gida sai tsakar dare, wanda hakan ke hanashi taɓuka komai a gidan.
Ta kuma ƙara da zargin Mijin nata da lakaɗa Mata duka, a gaban yaranta.
“Mijina ya na cin zarafina, tare da zagina a gaban yaranmu, har marina ma ya ke yi akan ɗan abu kaɗan.” a cewarta.
Matar ta buƙaci Kotun da ta raba Auren, tare da bata damar cigaba da kulawa da yaran da su ka haifa.
A nasa ɓangaren, Matthias, wanda shi ma ɗan ƙasuwa ne, ya musanta zarge-zargen.
Alƙaliyar Kotun, Thelma Baba, ta shawarci Ma’auratan da su sasanta junansu, tare da ɗage cigaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 31 ga watan Janairun da mu ke ciki, domin jin sakamakon sasancin na su.