Wata Mata Ta Haihu A Banɗaki, Ba Tare Da Tasan Tana Da Ciki Ba
Wata mata mai shekaru 34 a duniya, Marla McEntire, da ke ƙasar Georgia, ta bayyana yadda ta haihu a banɗaki, bayan da naƙuda ta kamata, ba tare da tasan ita ce ba.
McEntire dai, na ɗauke da ciki har na tsawon makonni 40 ne, ba tare da ta sani ba, duk kuwa da cewar, ta na kan tsarin tazarar Iyali.
Inda ta ce, sau ɗaya kawai ta yi ɓatan wata, a tsawon wannan lokaci, amma sai dai lamarin ya bata mamaki, a lokacin da ta yi awon ciki, a cewar jaridar Dailymail, ta ranar Litinin.
Daga bisa ni kuma, matar ta haifi Jaririnta mai tsawon ƙafa biyar, wato inci 18, wanda aka sanyawa suna, Atlas Cohen, a banɗaki.
Marla, ta kuma yaɗa labarin nata ne, a kafar sadarwa ta Tiktok, ta na mai cewar, ”Ina da shekaru 34, ban kuma taɓa tsammanin ina da ciki ba, a baya.
”Na samu ciki, a watan Mayun shekarar da ta gabata, kuma ban ga alamarsa ba, domin ko kaɗan cikina bai yi tudu ba, cibiyata bata fito ba, ban yi laulayin safe ba, ban taɓa jin komai ba.
”Kwatam wajejen Janairu, sai na fara jin ciwo kaɗan-kaɗan, a cikina, dan haka sai na garzaya wurin Likita, ba tare da kowa ya yi tsammanin cikine da ni ba.
”Ran nan kawai sai naƙuda ta kamani. Na cewa Mahaifina ya je ɗakin ajiya, ya ɗaukomin laxatives, ya yin da ni kuma na yi ta safa da marwa a banɗaki, har sama da sau biyar.
”A na biyar ɗin ne kuma, aka haifi Atlas”.