Wata Uwa Ta Gurfanar Da Ɗanta Da Ake Nema Ruwa A Jallo, A Gaban Rundunar Ƴan Sandan Kano
Mahaifiyar wani matashi mai laƙabin, Hantar Daba, wanda ya kasance guda daga cikin mutanen da rundunar ƴan sandan Kano ta ayyana nema ruwa a jallo, ta miƙa matashin ga rundunar ƴan sanda.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, shi ne ya bayyana hakan, ta cikin wani jawabi da ya fitar, a birnin Kano.
A cewar sa dai, rundunar ƴan sandan Kano, ta sanya tukuicin Naira 500,000 ne ga duk wanda ya gano inda za a riski Hantar Daba ɗin.
Kiyawa, ya kuma buƙaci dukkannin waɗanda su ke da ƙorafi akan Hantar Daba ɗin da su garzaya helikwatar rundunar ƴan sandan jihar.
SP Abdullahi, ya bayyana cewar Matashin ya nuna nadamarsa ƙarara kan abubuwan da ya aikata, tare da bayyana shirinsa na bada gudunmawa wajen farfaɗo da zaman lafiya, da cigaban jihar.
A yanzu kuma, Hantar Daba ɗin ya na hannun rundunar ƴan sandan Kano, inda ake cigaba da gudanar da bincike.