WOFAN Ta Ɗauki Sababbin Ma’aikatan Bunƙasa Noma 500
Ƙungiyar Mata Manoma ta ƙasa, WOFAN, ta gudanar da bikin ƙaddamar da ayyukanta na shekara ta biyu, da ɗaukar maíkatan bunƙasa ayyukanta kimanin 500, tare da raba Manyan Wayoyin Android guda 500, da Naúrorin Caji na Power Banks, ga sababbin maáikatan, domin samun gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
Manema Labarai sun rawaito cewa, wayoyin ƙirar Android, waɗanda sababbin jamián za su yi amfani da su wajen tattara bayanai, an sanya musu Manhajar da za ta iya ƙididdiga amfanin gonar da za a iya samarwa, tare da sarrafawa.
A jawabinsa, ya yin ƙaddamar da aikin, Shugaban kwamitin bada shawarwari kan gudanar da ayyukan ƙungiyar ta WOFAN, Farfesa Sani Miko, ya bayyanawa sababbin maáikatan da ƙungiyar ta ɗauka cewar, a halin da ake ciki fatan da ake da shi na samun tsaro a Najeriya ta fuskar abinci, ya dogara ne da ƙoƙarin su, duba da fatan da ake da shi na ganin ayyukansu sun bunƙasa amfanin da manoman ke iya samarwa.
A nata jawabin, Babbar Daraktar ƙungiyar ta WOFAN, Hajia Salamatu Garba, ta bayyana cewar za a horas da sababbin Jamián kan fannoni daban-daban na bunƙasa samar da amfanin gona, da sarrafa shi, da nufin bunƙasa abin da ƙananan manoma ke samarwa, ta hanyar bawa ɗai-ɗaiku da ma ƙungiyoyinsu horo, da tallafi kan yadda ayyukansu za su bunƙasa.