Rahotanni

YADDA AKA YI MIN DUKAN KAWO WUƘA, A BAKIN AIKI – EDITAN RARIYA ONLINE

Ni Ɗan Jarida ne, Ina Aiki Da Jaridar Yanar Gizo ta Rariya Online.

Ranar Lahadin da ta gabata, 21 ga watan Janairun da mu ke ciki, da misalin ƙarfe 8 da mintuna 49 na safiya, na samu labarin cewa, “Wani Kirista, Ya Kashe Musulmi (Tuƙur), da su ke Aiki a kamfanin FasAgro, da ke Zone 5 – Sharada Phase III, da misalin ƙarfe 8 da mintuna 30 na safiyar ranar. Hakan ya sa na garzaya farfajiyar kamfanin domin farautowa mabiyan Jaridata labarin abin da ke faruwa.

Zuwana wurin ke da wuya, na fara tattara bayanan sauti, ta hanyar tattaunawa da mutanen da su ke tsaye cirko-cirko a wurin. Bayan kammala hakan ne kuma, ganin cewa, da Jami’an Ƴan Sanda a wurin, cikin ƙwarin guiwa na ƙarasa inda gungun mutanen da su ke bakin ƙofar kamfanin su ke.

Da zuwana kuma, sai na iske su na jefa duwatsu cikin kamfanin, tare da ikirarin cewa, za su ƙona kamfanin, idan har ba a futo musu da wanda ya yi kisan, su ma sun kashe shi ba.

Na duba dama da haguna, na ga kamar babu wanda hankalinsa ya ke kaina, sai kawai na fito da wayata, na ɗauke su a hoto, tare da haɗawa da gajeren bidiyo.

Ina yunƙurin mayar da wayar cikin aljihuna ne kuma, sai wani ya lura da abin da ke faruwa, nan da nan ya kwarmatawa sauran mutanen cewa, na ɗauke su a bidiyo.

Kan Kace Kwabo, sai ga su sun yo kaina, ya yin da ni kuma nake ta kici-kicin fito da katin shaidata na Aikin Jarida, amma haka su ka rufeni da duka, duk kuwa da bayyana musu cewar, “Ni Ɗan Jarida ne” da na ke yi.

In taƙaice muku labari dai, a nan su ka yi min dukan kawo wuƙa, su na ta yunƙurin ƙwace wayata, nima ina ja.

• Sun fasa min waya.

• Sun fasa wani sashe, na Computer ɗin da ke cikin jakar bayana.

• Sun yayyaga min riga.

Haka mu ka yi ta kacaniya da su, har mu ka ƙarasa wurin motar Ƴan Sandan da ke wurin, a nan ne Jami’an Ƴan Sandan su ka bani kariya.

Ina jikin Motar Ƴan Sandan aka lalubo min Card Holder ɗina (Jakar zuba ID Cards), sannan Jami’i ɗaya ya rakani zuwa cikin unguwa. Amma hula da takalmana kam, shikenan sun ɓace a wurin.

****************************

Godiya Ta Musamman Ga Maigirma CEO : Alhaji Sani Ahmad Zangina.

Ƙarin Godiya Ga:

• Sabi’u Ɗanmudi Alkanawi (Mikiya Editor).

• Barista Ibrahim Assalafy (Legal Practitioner).

• Ismail Aliyu Ubale (CEO Albadar Ltd).

• Abubakar Yakasai (Vision FM).

• Bilal Muhammad Bello.

• Sani Abdullahi Samegu (BUK FM).

• Al-amin Usman Abubakar (BUK FM).

• Bashir Ahmad Dandago.

• Fiddausi Muhammad Jibrin (Jannat).

• Abdullahi Gulu.

• Adamu Abubakar Malte.

• Da kuma shugaban ƙungiyar Ɗaliban Najeriya, da ke karatu a ƙasar Nijar.

INA GODIYA MATUƘA, GA DUKKANNIN WAƊANDA SU KA KIRANI, A LOKACIN DA BANA IYA ƊAGA KIRAN (Na Samu Missed Calls 124, tare da tarin Messages).

MIFTAHU AHMAD PANDA (Sunana).

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button