Ilimi

YADDA AKE RIJISTAR JAMB UTME (MATAKI BAYAN MATAKI)

• Bayan Ɗalibi, ya buɗe JAMB Profile, tare da mallakar Profile Codes, abu na farko da ya kamata ya yi, shi ne ya garzaya JAMB CBT Centre mafi kusa da shi, ɗauke da lambobin Profile Codes ɗin da aka turo masa; sakamakon kammala sakandire (idan ba awaiting result bane); da kuma kuɗin rijista Naira 6,200 (ga Ɗaliban da basa sha’awar rubuta jarrabawar Mock), ya yin da waɗanda ke son rubuta Mock kuma, za su je da Naira 7,700.

• Idan Ɗalibi ya je CBT Centre zai bada kuɗin rijistar da ya je da su, da kuma Profile Codes ɗin da aka turo masa ta Message, inda a nan ne za a yi amfani da lambobin wajen saya masa lambobin ePIN.

• Bayan an saya wa Ɗalibi ePIN, za a bashi JAMB Form ya cike bayanansa, wanda ya ƙunshi rukunoni biyar (A,B,C,D & E).

Bari mu ga bayanan da ake buƙata, a kowanne rukuni :

<RUKUNIN A> :

• Cikakken Suna.

• Kwanan Watan Haihuwa.

• Lambar Waya.

• Ƙaramar Hukuma.

•Jiha.

• Ƙasa.

• Profile Codes.

• ePIN.

<RUKUNIN B>

• Akwai Buƙata Ta Musamman ?, Ko Babu ?.

• Adireshin Ɗalibi.

• Jiha, Da Garin Da Ɗalibi Ya Ke Son Rubuta Jarrabawarsa.

• Ɗalibi ya na da sha’awar rubuta jarrabawar MOCK, ko A’a ?.

<RUKUNIN C>

A nan ne Ɗalibi zai zaɓi makarantu huɗu da ya ke so, tare da Courses ɗin da ya ke son karantawa, a makarantun (1st Choice, 2nd Choice, 3rd Choice, & 4th Choice).

Abin Lura: Ba lallai sai Jami’a Ɗalibi zai iya cikewa ba, A’a kowanne Ɗalibi ya na damar cike Jami’a, Kwalejin Ilimi, Kwalejin Fasaha (Polytechic), ko Monotechnic.

<RUKUNIN D>

A nan ne Ɗalibi zai zaɓi darussan da ya ke son rubutawa a jarrabawarsa ta JAMB (Subject Combination).

Akwai buƙatar Ɗalibi ya nutsu sosai, wajen zaɓar Subjects Combination ɗinsa, domin kuskure a wannan mataki ya kan iya hana Ɗalibi samun Admission, duk yawan makin da ya samu a JAMB kuwa.

DUKKANNIN ƊALIBAN DA KE SON SANIN HAƘIƘANIN SUBJECTS COMBINATION ƊIN COURSE ƊIN DA SU KE SON CIKEWA, SU TUNTUƁI WANNAN LAMBAR : 08039411956.

<RUKUNIN E>

Abin da ake buƙatar cikewa a wannan rukuni na E shi ne, sakamakon kammala Sakandire ɗin Ɗalibi, wanda ya haɗarda :

• Nau’in jarrabawar da ya yi (NECO, WAEC, NABTEB, ko NBAIS.

• Sunan Makarantar da ya yi jarrabawar.

• Shekarar da ya yi.

• Ta gwamnati ce, ko ta kuɗi ?.

• Da kuma lambar rijista (Registration Number).

∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆∆

Bayan Ɗalibi, ya cike dukkannin waɗannan bayanai, a jikin Form ɗin da za a bashi, Jami’an CBT Centre ɗin da ya halarta, za su shigar da bayanan a shafin hukumar JAMB; Sannan su ɗauki hoton ɗalibin; tare da Thumprints ɗinsa.

BAYAN ƊALIBI YA KAMMALA DUKKANNIN WAƊANNAN MATAKAN, SHIKENAN! YA KAMMALA RIJISTAR JAMB UTME.

√• Kafin Ɗalibi Ya Bar CBT Centre : ZA A BASHI REGISTRATION SLIP, NOVEL, DA CD.

Ga masu tambaya, ko neman shiga ASOF JAMB GROUP, kaitsaye su tuntuɓi wannan lambar : 08039411956.

Rubutawa : Miftahu Ahmad Panda.

08039411956.

Miftahu Ahmad

Miftahu Ahmad Panda (Babban Editan Rariya Online), Ɗan Jarida ne, kuma Marubuci, da ke da ƙwarewa a fannonin Tattara Labarai, Fassarawa, Samar Da Rahotanni, Da ma Tacewa. Kafin kasancewarsa a wannan matsayi kuma, ya yi Aiki Da Gidajen Jaridu Da Dama, Har ma da Tashar Radio. 08039411956.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button